Mukamin Imam Sadik (a.s) Na Ilmi:

________________________

Imam Sadik (a.s) ya ci gaba da rayuwarsa cikin irin wannan yanayi na yaduwar ilmi da bayyanar mazhabobi, inda ya gudanar da ayyukan da suka hau kansa na wayar da kan al'umma da kuma karantar da su hakikanin addinin Musulunci a matsayinsa na jagora, malami, mai shiryarwa kana kuma wanda dukkan malamai suke komawa gare shi.

Kamar yadda dai muka sani, Imam Sadik (a.s) ya samo ilminsa ne daga iyayensa, daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a). Tun a lokacin zamanin mahaifinsa, Imam Bakir (a.s), ya taimaka masa wajen assasa jami'ar Ahlulbaiti (a.s) a masallacin Annabi mai girma, suna masu watsa ilmi tsakanin malaman fikihu, tafsiri, hadisi da dai sauran ilmummuka. Manyan malumma sun kasance suna yin tururuwa zuwa wajensu don sha daga taskarsu ta ilmi, ta yadda ba su samu ilmin Musulunci da suka hada da ilmin tafsiri, hadisi, fikihu, akida da dai sauransu ba daga wani malami daga cikin malaman Musulunci ba kamar yadda suka samu daga wajen Imam Bakir da Sadik (a.s) ba.

Allama Sayyid Muhsin al-Amin ya ce: "Hafiz bn Ukdah al-Zaidi cikin littafin maruwaita hadisinsa ya ambato tabbatattun mutane dubu hudu da suka ruwaito hadisi daga Ja'afar bn Muhammadu.... (1)".

Haka nan ya ruwaito cewa: "Najashi cikin littafin maruwaita hadisinsa ya ruwaito daga Hasan bn Ali al-Washa' cikin hadisinsa cewa; 'Na riski malamai dari tara a wannan masallaci (wato Masallacin Kufa) wadanda suke cewa Ja'afar bn Muhammadu ya gaya min".

Hasan bn Ziyad yana cewa: "Na jiyo Abu Hanifa, yayin da aka tambaye shi kan wane ne ya fi ilmi daga cikin malumman da ya gani, sai ya ce: Ja'afar bn Muhammad".

Malik bn Anas yana cewa: "Ido bai taba gani ba kamar yadda kunne bai taba ji haka nan wani mutum bai taba zuwa ga zuciya ba da ya fi Ja'afar al-Sadik falala, ilmi, ibada da tsantsaini ba(2)".






____________
1- A'ayan al-Shi'a na Muhsin al-Amin, juzu'i na 1, shafi na 661.

2- Al-Manaqib na Ibn Shahr Ashub, juzu'i na 4, shafi na 247.