Haihuwar Imam Ja'afar bn Muhammad al-Sadik (a.s):

________________________

An haifi Imam Ja'afar bn Muhammadu al-Sadik (a.s) ne a garin Madina a ranar goma sha bakwai ga watan Rabi'ul Awwal shekara ta tamanin da uku da hijirar Ma'aiki (s.a.w.a).

Imam Sadik (a.s) dai ya rayu ne karkashin kulawar kakansa Imam Sajjad (a.s) da mahaifinsa Imam Bakir (a.s), inda ya sha daga taskansu ta ilmi.

Don haka Imam Sadik (a.s) tare da iyayensa tsarkaka sun kasance igiya mai karfi da take ci gaba da yaduwa har zuwa ga Ma'aikin Allah (s.a.w.a), har ila yau kuma ta kasance wata rayayyiyar makaranta da Musulunci ya dogara da ita wajen tabbatar da hukumce-hukumcensa da kuma kiyaye akidunsa. Imam Sadik (a.s) ya yi bayanin wannan lamari yayin da yake cewa:

"Mahaifina ya gaya min wani hadisi, hadisin kuwa daga kakana ne, hadisin kakana din kuwa daga Aliyu bn Abi Talib ne, hadisin Aliyu bn Abi Talib kuwa hadisin Manzon Allah (s.a.w.a) ne, hadisin Manzon Allah (s.a.w.a) maganar Allah ne Madaukakin Sarki(1).

Limaman Ahlulbaiti (a.s) dai sun gaji ilmi ne da daga mahaifinsa har zuwa ga Aliyu bn Abi Talib (a.s), wanda Manzon Allah (s.a.w.a) dangane da shi ya ke cewa: "Ni ne birnin ilmi, Aliyu kuma kofarsa(2)". Ta haka kuma yake karewa zuwa ga Manzon Allah (s.a.w.a) don kuwa shi ne magajin ilmi da masaniyarsa.

Daga nan za mu iya fahimtar cewa Imam Sadik (a.s) ya samo Musulunci daga tushensa kamar yadda aka saukar da shi ga Ma'aikin Allah kana kuma ya isar da shi. Hakan ne ya sa ma malamai daga ko ina suke tuttudowa zuwa gare shi suna masu kwadayin ilmi da falalarsa, ta yadda adadin dalibansa da suka sha daga gare shi kana kuma suka isar da ilmi zuwa ga bangarori da dama na duniya suka kai dubbai. Don haka Imam Sadik (a.s) ya kasance mai raya sunnar Manzo da kuma jaddada ilmin shari'ar Ubangiji.

Imam Sadik (a.s) dai saboda shiriyar da take tare da shi da kuma hasken Musulunci da ke tare da shi ya zamanto abin da ke janyo hankulan mutane zuwa gare shi, wannan lamari kuwa ya ba shi damar kiran mutane zuwa ga sakon Musulunci na hakika da kaurace wa duk wani abu maras tushe.

Imam Malik bn Anas (daya daga cikin limaman Ahlussunna) na cewa: "Ja'afar bn Muhammadu ya kasance mutum ne mai yawan murmushi da sakin fuska, idan aka ambaci Manzon Allah (s.a.w.a) sai launinsa ya canza, kuma ban taba ganinsa yana fadin hadisan Ma'aiki ba face sai yana cikin tsarki (alwala). Na kasance ina tare da shi tsawon lokaci amma ban taba ganinsa ba face cikin daya daga cikin wadannan yanayi: Ko dai yana salla, ko ya yi shiru ko kuma yana karanta Alkur'ani mai girma. Ba ya tsoma baki cikin abin da bai shafe shi ba, kuma yana daga cikin malamai da masu ibadan da suke jin tsoron Allah a ko da yaushe(3))".

Ibn Abi Umair yana cewa: "Na ji Malik bn Anas, malamin fikihun garin Madina, yana cewa: '…ya kasance mai yawan ruwaito hadisai, mai dadin zama kana kuma wanda ake yawan amfanuwa da shi….

Wata shekara na yi aikin hajji tare da shi, a duk lokacin da ya fara yin Talbiyya (wato fadin: Labbaika allahumma Labbaik…(na amsa maka Ya Allah na amsa maka)…) sai sautinsa ya yanke daga makogoronsa kamar zai fado daga abin hawansa, sai na ce masa: 'Ka fadi Ya dan Manzon Allah! Lalle dole ne ka fadi, sai ya ce: "Ya Ibn Abi Amir! Ya ya zan rufe ido in ce: Labbaika allahumma Labbaik, ina tsoron kada Allah Madaukakin Sarki Ya ki karban wannan amsa nawa(4)".






____________
1- A'ayan al-Shi'a na Muhsin Amin, juzu'i na 1, shafi na 664.

2- Al-Mustadrak na Hakim, juzu'i na 3, shafi na 126, Usadul Gabah na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 22 da Jami' al-Saghir na Suyuti, shafi na 364

3- Al-Tawassul wa al-Wasilah na Ibn Taimiyya, shafi na 52, an naqalto daga littafin Imam Sadiq wa Mazahib al-Arba'.

4- Al-Khisal na al-Saduq, babi na uku, hadisi na 219.