Babu wani mutum guda a zamanin Imam Sadik (a.s) da ya samu matsayin da yake da shi. Don kuwa dukkan al'umma suna ganinsa ne a matsayin jigon gidan annabci da Ahlulbaiti kana kuma alama sannan jagoran fada da zalunci da babakeren Umayyawa da Abbasiyawa, haka nan kuma so da kaunarsa wajibi akan dukkan al'umma kamar yadda Allah Madaukaki yake cewa:
"Ba na tambayarku wata lada a kansa face dai soyayya ga makusanta …". . (Surat al-Shurah: 23)
Zalunci Umayyawa da ta'addancinsu dai ya karu a zamanin Imam Sadik, wato kusan karshe lokacin mulkinsu, don haka gabar da al'umma suke musu ya kara tsananta, to sai dai kuma sanannen abu cewa a daidai lokacin kaunar mutane ga Ahlulbaiti kuma sai dada karuwa take yi.
Hakan ne ma ya janyo aka fara samun yunkuri da sunan Ahlulbaitin wajen fuskantar sarakunan Umayyawa da fatattakansu. Masu wannan yunkuri dai suna rera taken kare Ahlulbaiti da kuma kwato halifanci da mai she shi ga asalin masu shi wadanda suka cancance shi, wato Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a). To sai dai kuma Imam Sadik (a.s) bai kusanci wannan yunkuri ba saboda ya riga da ya san sakamakon da zai haifar daga karshe, ya riga da ya san babu gaskiya cikin wannan ikirari na masu yunkuri, ya riga da ya san cewa bayan masu wannan kira (Abbasiyawa) sun sami mulki su ma za su cutar da Ahlulbaitin.
Don haka ne ya ja kunnen mabiyansa da su guji kusantan wannan yunkurin.
Tarihi ya ruwaito cewa wata rana daya daga cikin fitattun mutanen da suka jagoranci wannan yunkuri na yin waje da Umayyawa wato Abu Salma al-Khallal ya aike da wasika zuwa ga Imam Sadik (a.s) yana mai neman izinin ya yi wa Imam din bai'a a matsayin halifan musulmi, amma sai Imam (a.s) ya kona wannan wasika ba tare da ya amsa wannan bukata ba. Daga nan sai ya ce wa wanda ya kawo wasikar: "Tafi ka gaya wa wanda ya aiko ka abin da ka gani".
Wannan dai yana nuni da inda wannan yunkuri ya sa gaba ne, kuma haka aka ci gaba da gabatar da irin wannan bukata ga Imam Sadik din amma dai ko da sau guda bai amince ba.
Irin matsayin da Imam Sadik (a.s) yake da shi ne ya sanya al'umma suke ta komawa gare shi don fatattakan Umayyawa da suka ishi kowa, to sai dai ya riga da ya san cewa fahimta da wayewar al'umma din ba ta kai matsayin da za a iya dogara da ita ba, a bangare guda kuma ya san cewa akwai wata manufa da wasu 'yan siyasa suke son cimmawa ta hanyar wannan kira ta su. Don haka ne ya ki amincewa da wannan bukata ya kuma ba da muhimmanci wajen karfafa akida da fahimtar mutane a matsayin abin da aka fi bukata a lokacin.
Abin da Imam (a.s) din yake gudu kuwa da jan hankulan mutane dangane da shi, shi ne ya faru.
____________