Bisa la'akari da cewa Imaman Ahlulbaiti (a.s) don daga na farkonsu har zuwa na karshensu, su ne za su kasance shuwagabanni kana kuma masu shiryar da mutane a lokacin Imamancinsu zuwa ga tafarkin gaskiya da Manzon Allah (s) ya zo da shi, don haka dole ne su sami tarbiyya ta musamman daga wajen iyayensu ko kuma masu kula da su (kamar yadda ya faru da Imam Ali da kuma Imam Husaini (a.s) wato yadda Manzon Allah (s) ya kula da Imam Ali (a.s) duk da cewa ba shi ne mahaifinsa ba, haka nan kuma kamar yadda Imam Hasan ya kula da Imam Husaini, bayan rasuwar mahaifinsu duk kuwa da cewa ba shi ne ya haife shi, to amma a lokacin akalar kula da dukkan al'umma tana wuyarsa ne).
Don haka ne wadannan Imamai suke samun irin wannan tarbiyya daga wajen mahaifan nasu ko kuma masu kula da su din tun suna kanana (hakan kuwa baya ga irin shiryarwa ta Ubangiji ta musamman ne da take samunsu wacce kuma take tare da su tun ranar da aka halicce su har zuwa lokacin da suka koma ga mahaliccinsu, Madaukakin Sarki.
Imam Ridha (a.s) dai ya tashi ne da kuma girma a karkashin kulawan mahaifinsa Imam Kazim (a.s) har na tsawon shekaru 35 kafin Mahaifin nasa ya yi shahada. A yayin wannan lokaci dai Imam Ridha ya sami tarbiyya da kula irin ta Imamanci daga wajen mahaifin nasa, bugu da kari kan dimbin ilmi da kyawawan dabi'u da ya samu daga wajen mahaifin nasa (a.s). Hakan kuwa saboda kasancewa shi ne zai zamanto shugaba kana mai shiryar da al'umma bayan mahaifinsa (a.s). Ta haka ne ya zamanto malami, mafi sani da kyawawan dabi'u a lokacin Imamancinsa.
Saboda irin wannan tarbiyya da Imam Ridha ya samu daga mahaifinsa da kuma sanin cewa shi ne Imami na gaba wanda zai gaji wannan nauyi na shiryar da al'umma, ya sa mahaifin nasa bai yi wata-wata ba ya fara gabatar da shi a gaban mabiyansa na wancan lokacin da cewa shi ne wanda zai gaje shi bayan shahadarsa. Hakan kuwa saboda wasu dalilai ne da suka hada da cewa Imam Kazim ya yi hakan ne don ya sanar da mutane da wuri kan wanda zai gaje shi, da kuma hana faruwar wani rikici da ka iya tasowa daga baya da kuma rufe kofa ga duk wani wanda yake so ya yi ikirarin cewa shi ne Imam bayan Imam Kazim din kamar yadda ya faru a lokacin wasu Imaman.