SHAHADAR IMAM RIDHA (A.S)

Bisa la'akari da cewa da wuya dukkan duk wani abin da aka yi shi ba don Allah ba kana kuma da nufin cutar da al'umma da kuma addinin Allah din ya yi karko, don haka wannan buri na Ma'amun dai bai cika ba don kuwa burinsa na samun sakat kana kuma mutane su kyamaci Imam Ridha bai cika ba, face ma dai mutanen sun ci gaba ne da son Imam din da kuma komawa gare shi. A takaice dai adadin 'yan shi'a sai dada karuwa ya ke yi, wanda hakan ya dada sanya Ma'amun cikin damuwa da kuma rashin sanin abin yi.

Faruwar wannan lamari dai ya sa Ma'amun ya gane cewa ya yi babban kuskure wajen nada Imam din a matsayin wazirinsa mai jiran gado. Don haka sai ya fara tunanin yadda zai kawar da Imam da kuma kashe shi don ya huta daga wannan damuwa da yake ciki kamar yadda yake tunani.

Daga karshe dai Ma'amun ya yanke shawarar kashe Imam Ridha (a.s), inda ya sa masa guba cikin inabi ya tilasta wa masa sha. Bayan wannan lamari Imam ya dawo gida, ya umarci daya daga cikin manyan sahabbansa Aba Salat da ya dauke shimfidan da ke dakinsa, kuma kada ya bar wani ya shigo cikin dakin saboda lokacin ne zai cika. Imam ya ce yana so a daka shimfidan ne don ya rasu a kan kasa kamar yadda kakansa Imam Husaini (a.s) ya rasu. Da man kafin faruwar wannan lamari, Imam Ridha (a.s) ya yi mafarki inda ya Manzon Allah (s) yana ce masa: "Gobe ka zo wurinmu, don abin da muka tanadar maka a nan yafi halin da kake ciki a halin yanzu".

Don haka Imam Ridha (a.s) ya yi shahada ne a ranar 30 ga watan Saffar, shekara ta 203 hijiriyya yana dan shekara 55 a duniya. Kuma an bisne shi ne a kusa da inda aka bisne Harun al-Rashid a garin Masshad dake Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Bayan shahadar Imam Ridha (a.s) dai al'umman sun ta bore da nuna kiyayya ga Ma'amun wanda suke ganin shi ne ya kashe Imam din, ta yadda har da Ma'amun din ya yi hayan wasu mutane don su yi yawo tsakanin al'umma da nuna musu cewa ba shi da hannu wajen kashe Imam. To amma dai duk da hakan hakarsa ba ta cimma ruwa ba don da dama daga cikin mutanen sun ki yarda da hakan. Daga karshe dai rayuwa ta yi masa kunci kwarai da gaske har lokacin da ya mutu cikin mummunan yanayi. "Hakan shi ne sakamakon wadanda suka yi zalunci"  (Surar Ma'ida 5:29)