HAIHUWAR IMAM RIDHA (A.S):

An haifi Imam Ridha (a.s) ne a ranar 11 ga watan Zil-Ka'ada shekara ta 148 bayan hijira Manzon Allah (s) a birnin Madina, Mahaifansa su ne Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s), Imamin Shi'a na bakwai, mahaifiyarsa kuwa ita Najma, wacce ta kasance mace ce mai tsarki da kuma tsoron Allah, Madaukakin Sarki.

Tun yana karami dai Mahaifinsa Imam Musa al-Kazim (a.s) ya fara gabatar da shi ga mabiyansa a matsayin Imamin da zai gace shi bayan shahadarsa. Don haka ya ci gaba da karantar da shi da kuma shiryar da shi hanyoyi da kuma tafarkin Kakanninsa (a.s) don ya samu daman jagorantar al'umma da kuma shiryar da su bayansa kamar yadda sauran kakanninsan suka yi kuma jikokinsa ma za su yi a bayansa.

Don cimma wannan manufa ce ma aka ruwaito daya daga cikin na kurkusa da Imam Kazim din wato al-Makhzoomi yana cewa: "Wata rana Imam Kazim (a.s) ya tara mu kana ya ce mana: "Na tara ku ne don sanar da ku kana kuma ku shaida cewa wannan (wato Imam Ridha) shi ne wasiyyi na kuma magajina a bayana". To bayan wannan sanarwa, kana kuma saboda la'akari da irin halin da ake ciki a lokacin na farautar 'ya'yan gidan Manzon Allah da kuma kashe su, bisa zalunci da nufin dushe hasken Musulunci na hakika da sarakunan zalunci na wancan lokacin suke yi ya sa Imam Kazim (a.s) ya ci gaba da gaya wa mabiyan nasa cewa: "Wannan magana da na gaya muku ku rike ta kada ku bari wani ya santa in ba wanda kuke da yakini kan cewa shi daya ne daga cikin abokanku kana kuma mabiyina na hakika ba.