A lokacin Imamancin Imam Ridha (a.s) an samu karuwar 'yan shi'a da kuma yaduwar koyarwar Ahlulbaiti (a.s) bugu da kari kan tawaye da bore-boren 'yan shi'a da aka dinga samu don nuna rashin amincewa da mulkin danniya irin ta Abbasiyawa, don haka ne sarki Ma'amun (halifan Abbasiyawa) ya fara tunanin neman mafita daga wadannan matsaloli da ya samu kansa a ciki, wanda kuma mulkin iyaye da kakanninsa suka gagara magancewa. Don haka sai ya fara tunanin zaban Imam Ridha (a.s) a matsayin wazirinsa wanda kuma zai gaje shi bayan ya mutu, hakan kuwa da nufin cimma wasu burori nasa ne guda biyu:
Na farko dai shi ne don ya kawo karshe da kuma hana tawayen da zuriyar Manzon Allah (s) da mabiyansu suke wa gwamnatinsa, don kuwa suma (Ahlulbaitin) za su kasance cikin gwamnatin kenan kana su kuma mabiyansu ba za su so su yi tawaye wa shuwagabanninsu ba.
Na biyu kuma shi ne su sa kaunar da mutane suke wa Imam Ridha (a.s) ta ragu saboda Ma'amun din zai yi kokarin ya sanya Imam din ya shiga dumu-dumu cikin harkokin duniya da na mulki, wanda hakan zai sa mutane su juya masa baya da kuma kyamansa saboda ya zamanto kamar su Ma'amun din kenan da sauran iyayensa da kakanninsa da suka gabata, (hakika Imam ya nesanta daga hakan).
Har ila yau kuma Ma'amun ya riga da ya san cewa ba zai jima yana mulki ba matukar dai bai nuna yana tare da Imam Ridha (a.s) ba, haka nan kuma masu ba shi shawara da masu leko masa asirai sun tabbatar masa da hakan.
Don haka sai Ma'amun ya yanke shawarar gabatar da wannan bukata ga Imam Ridha na zama wazirinsa, inda ya tilasta wa Imam din zuwa fadansa don tattaunawa da shi kan wannan batu.
Ma'amun dai mutum ne mai wayo tsiya, don haka koda zuwan Imam fadarsa, sai ya tarbe shi hannun bibbiyu da kuma kyautata masa. Kana daga baya sai ya ce masa: "Ina so ne in sauka daga karagar mulki in mika ta gare ka". Amma sai Imam Ridha (a.s) ya ki amincewa da wannan bukata. Ganin haka sai Ma'amun ya ce wa Imam to idan ba zai amince da wannan matsayi ba, to ya yarda ya zamanto wazirinsa wanda zai gaje shi bayan ya mutu. Nan ma dai Imam (a.s) ya ki amincewa. Don haka sai ya zamanto Ma'amun ba shi da wata mafita wajen cimma wannan buri nasa face dai ya yi amfani da karfi wajen tilasta wa Imam yarda da wannan bukata, don haka sai ya fito fili ya nuna wa Imam cewa dole ne fa ya amince da wannan bukata ko kuma ya kashe shi, yana mai cewa:
"Umar bn Khattab ya nada kwamiti na manya kasa don su zabi halifa, a cikinsu kuwa akwai kakanka, Amirul Muminina, Aliyu bn Abi Talib. A yayin nadin wannan kwamiti, Umar ya shardanta cewa don wanda ya ki amincewa da abin da aka tsayar to a kashe shi. Don haka babu wata mafita gare ka face dai ka yarda da wannan bukata".
Ganin yadda yanayin ya kasance, sai Imam Ridha (a.s) ya amince da wannan bukata, yana mai cewa: "Zan amince da wannan bukata taka amma bisa sharadin cewa ba zan ba da wani umurni ba, haka nan kuma ba zan yanke hukumci ba, ba zan nada wani mutum (akan wani matsayi ba) kuma ba zan saukar da shi ba (daga matsayin), haka nan kuma ba zan canza komai ba daga abubuwan da suke a halin yanzu ba". Ma'amun dai ya amince da wannan sharudda na Imam, sai aka tsayar da ranar da za a sanar wa mutane wannan matsaya da kuma yin bai'a wa Imam (a.s).
Bari mu ji irin halin da Imam Ridha (a.s) ya kasance a ciki a wannan rana da jama'a za su yi masa bai'a:
Daya daga cikin makusanta Imam Ridha (a.s) wanda ya kasance a kusa da Imam din a wannan rana yana cewa: "A wannan rana na kasance a gaban Imam. Sai ya kalle ni alhali ina cikin farin ciki kan abin da ya faru (na nada Imam a matsayin yarima mai jiran gado). Sai ya min ishara da in matso kusa, sai na matsa kusa da shi sai ya ce min: 'Kada ka damu kanka da wannan lamari kuma kada ya sanya ka farin ciki. Don kuwa lamari ne da ba za a iya cimma manufa da shi ba".
Hakan kuwa saboda ilmin da Imam din yake da shi ne na dalilin da ya sa Ma'amun ya yanke wannan shawara na nada shi yarima mai jiran gadon da kuma abin da yake son cimmawa.
To sai dai kuma duk da wannan matsayi da ya samu, hakan bai rudi Imam ba da kuma sanya shi ya koma ga harkokin duniya da kuma jin dadi da mancewa da talakawa ba. Imam Ridha (a.s) ya ci gaba abin da ya saba na bautan Allah da taimakon marasa galihu. Haka nan kuma ya ci gaba da yada koyarwa irin ta Mutanen Gidan Manzon Allah (s) da kuma shirya zaman makomin Imam Husaini (a.s) hatta a fadar mulki.
Wata hanya kuma da Ma'amun din ya bi wajen dada sanya idanuwa a kan Imam Ridha (a.s) ita ce ta hanyar aurar masa da 'yarsa Ummu Habib duk dai da nufin nuna mika wuya da kauna ga Imam din don cimma wadannan burori nasa da muka bayyana a sama.