Imam Ridha (a.s) dai yana da karamomi da yawan gaske, to amma da yake shafin namu kadan ne, don haka a nan za mu kawo guda ne kawai daga cikin irin wadannan karamomi nasa.
Labarin da za mu kawo kuwa da ya ke tabbatar mana da karamar Imam din shi ne labarin wani mawaki mai suna Da'abal, wanda ya kasance ya kan rera wa Imam din waka.
An ruwaito Da'abal din yana cewa: "Lokacin da na shirya wata waka ina mai jinjina wa Ahlulbaiti (a.s), sai ya yanke shawarar tafiya Khorasan don karanta wakar wa Imam Ridha (a.s). Lokacin da na isa na karanta wannan waka ga Imam, sai ya kara wasu baitoci a cikinta da suke magana kan shahadarsa. Kana sai ya ce min: "Ka boye wannan waka taka kada ka karantata ga kowa". Bayan haka sai Ma'amun ya samu labarin isowa ta da kuma rera wannan waka da na yi a gaban Imam Ridha, don haka sai ya sa aka kira ni ya bukaci in rera masa wakar, amma dai na nuna masa babu wata waka tattare da ni, to amma duk da hakan dai ya kira Imam Ridha ya tilasta min karanta wannan waka a gaban Imam din.
Bayan da na karanta wannan waka, Ma'amun ya nuna alamun ya yi farin ciki da ita, don haka ya ba ni kyauta mai yawa da kuma doki. Shi ma Imam (a.s) ya bani dinar dari na kudin da Ma'amun ya sa aka sanya sunansa a jiki, yana (Imam) mai cewa: "Rike wadannan wata rana za ka bukace su".
Daga nan sai na roki Imam (a.s) da ya ba ni rigarsa don idan na mutu a yi min likkafani da ita, nan take kuwa Imam ya amsa min wannan bukata tawa ya bani rigar yana mai cewa: "Ka kiyaye wannan riga don ta hanyarta za ka tsira daga hatsari". Daga nan sai na kama hanyar komawa gida tare da wata tawaga da za ta tafi alhali ina kan wannan doki da aka ba ni kyautarsa.
A hanyarmu kuwa sai 'yan fashi suka bullo mana suka kwace dukkan abin da muke da shi, ba a jima ba sai na ga wani daga cikinsu wanda ya yi kama da babbansu yana haye a kan wannan doki nawa yana kuma rera wakar da na tsara. Sai na matsa kusa da shi na ce masa: "Shin ka san wanda ya tsara wannan wakar kuwa?". Sai ya ce ai Da'abal Khuza'i ne. Sai na ce masa ka san kuwa ni ne Da'abal din, sai ya yi mamakin hakan amma dai bai yarda ba. Sai na ce masa ya tambayi mutanen da muke tare da su, koda ya tambaye su sai suka tabbatar masa cewa ni ne Da'abal. Koda ya ji haka, sai ya umarci mutanen nasa da su dawo mana da kayayyakinmu da suka kwace. Wanda hakan ya yi daidai da fadin Imam Ridha (a.s) cewa wannan riga tasa za ta kasance min kariya kana kuma sanadin 'yantuwata". (Karama ta farko)
Bayan haka sai Da'abal ya ci gaba da tafiyarsa inda ya iso garin Kum. Lokacin da mutane suka sami labarin isowarsa sai suka tuttudo zuwa gurinsa da kuma son ya rera musu waka, inda ya yarda ya rera musu wakar, su kuwa suka tara masa kudi da dai sauran alherori. To sai dai kuma lokacin da suka ji labarin wannan riga ta Imam Ridha (a.s) sai suka bukaci ya sayar musu amma Da'abal yaki, suka bukaci to koda wani yanki na riga ya yarda ya sayar musu, hakan ma dai bai samu ba.
To bayan barinsa garin Kum, sai wasu matasa suka bi shi suka kwace wannan riga, suka dawo Kum din, nan take sai Da'abal ya biyo, ya bukaci su ba shi wannan riga amma dai suka ki, don haka dai da ya ga babu yadda zai yi sai ya bukaci to su ba shi wani yanki na rigar su kuma su rike saura. Sai suka yarda suka ba shi tare da kudade masu yawa, sai ya kama hanya zuwa gida.
Koda ya iso gida sai ya samu barayi sun yashe masa gida ba su bar masa komai ba. Daga nan sai ya tuna abin da Imam ya gaya masa a lokacin da ya ke ba shi Dinar darin nan cewa: "Rike wadannan (dinare) wata rana za ka bukace su". Don haka sai ya tafi kasuwa ya sayar da su da kudade masu yawa. (Karama ta biyu).
Bayan tafiyarsa kuma matarsa ta kamu da ciwon ido ta yadda har likitoci suka ce masa ba za ta warke ba daga wannan ciwo. Don haka sai ya dauki wannan bangare na rigar Imam Ridha (a.s) da mutanen Kum suka bar masa ya daure mata idon nata, koda gari ya waye sai ya ga ta warke kamar ba ta taba yin ciwon ba. (Karama ta uku)
To a cikin wannan labari dai mun ga kadan daga cikin karamomin Imam Ridha (a.s), muna rokon Allah da Ya arzurta mu da shiga cikin inuwa da damshin wannan Imami namu
abin koyi.