KADAN DAGA CIKIN KALAMAN IMAM RIDHA (A.S):

  1. Wanda ya dau lokaci da yin wahala wajen (rufa asirin) kansa da na iyalinsa kamar mutumin da ya yi Jihadi ne a tafarkin Allah.

  2. Duk lokacin da za ka kira sunan wani mutum, ka kira shi da girmamawa.

  3. Ka kiyaye tsabta, don tsabta na daga cikin halayen Annabawa.

  4. Mafi munin mutane shi ne, wanda kasantuwansa ba ta da wani amfani ga sauran mutane.

  5. Wanda ya cutar da musulmi, to ba ya daga cikinsu.

  6. Abokin mutum shi ne hikimarsa, kana jahilci kuma makiyinsa.