HIJIRAR IMAM RIDHA (A.S) DAGA MADINA ZUWA KHORASAN

A lokacin da Ma'amun ya gayyaci Imam Ridha (a.s) zuwa birnin Khorasan (Masshad) inda fadar mulkinsa take da nufin nada shi a matsayin yarimansa mai jiran gado, Imam Ridha (a.s) ya bar birnin Madinan Manzon Allah (s) inda ya bi ta garin Basra daga nan kuma ya shiga birnin Bagadada na kasar Iraki kenan kafin ya isa birnin Kum na Iran. Bayan isowarsa birnin Kum ya ya da zango na dan wani lokaci kafin ya ci gaba da wannan tafiya tasa da ba zai dawo daga ita ba.

A yayin wannan tafiya dai duk garin da ya bi ya kan sami kyakkyawan tarba daga wajen al'ummomin wadannan garuruwa wadanda suke kaunar Imam din da kuma bin koyarwarsa.

Isowarsa Birnin Nishabur

Birnin Nishabur dai yana daga cikin garuruwan da suke da dadadden tarihi a Iran, wanda kuma yake da mabiya Ahlulbaiti (a.s) da yawan gaske. Do haka Imam Ridha (a.s) ya samu gagarumar tarba daga al'umman wannan gari lokacin da ya iso wanda da wuya a iya kwatanta shi da duk wata tarba da ya samu.

A wancan lokacin dai garin Nishabur ya kasance gari ne da ke cike da malamai da maruwaita hadisai, don haka koda Imam Ya iso garin sai suka nufi wajensa da alkalumma da takardunsu don rubuta hadisai. Daga cikin maruwaitan da suka iso gun Imam din sun hada har da Muhammad bn Aslam Tusi, wanda ya kasance daga cikin manyan maruwaita. Sai ya bukaci Imam Ridha (a.s) da ya gaya wa mutane wani hadisi.

Sai Imam ya ce wa mutane "Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: KalmarLa-ilaha-illallah shinge (garkuwa) na ne, duk kuwa wanda ya shiga shingena ya tsira daga azaba ta, sai Imam ya sake juyowa ya ce "Amma fa da sharuddanta, ni kuma ina daga cikin sharuddan nata.

Daga nan sai Imam ya ci gaba da tafiyansa zuwa Khorasan.

A lokacin da Imam Ridha (a.s) ya iso garin Marwa, Ma'amun ya je ya same shi tare da manyan sarakuna da mataimakansa, inda suka tarbi Imam hannun bibbiyu. Daga nan kuma sai Ma'amun ya fara sanar da shi dalilin kiran nasa.