GABATARWA:

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah Muhammad al-Mustafa al-Amin da tsarkakan mutanen gidansa masu shiryarwa.

Imam Aliyu bn Musa al-Ridha dai shi ne Limamin Shi'a na takwas kana kuma ma'asumi na goma cikin Ma'asumai sha hudu da muke da su.

Shi dai shi ne dan Imam Musa al-Kazim bn Ja'afar bn Muhammad al-Sadik bn Muhammad bn Ali al-Baqir bn Aliyu bn Husaini al-Sajjad (Zainul Abidin) bn Imam Husaini bn Aliyu al-Shahid bn Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (Amincin Allah ya tabbata a gare su).

Don haka a takaice dai yana daga cikin zuriyar Manzon Allah (s) da Allah da ManzonSa suka yi magana a kansu da kuma daukaka matsayinsu zuwa ga matsayi na Isma' (rashin aikata sabo) don su zamanto abin koyi ga dukkan talikai.

An haife shi a garin Madina kana kuma ya yi shahada ne a garin Mashhad inda kuma aka bisne shi a gurin.

Amincin Allah Ya tabbata a gare ka Ya Dan Manzon Allah, ranar da aka haife ka, da ranar da ka yi shahada da kuma ranar da za a tashe ka kana rayayye.

ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN.