Lokacin Imamancin Imam Ridha (a.s) dai ya yi daidai ne da lokacin mulkin sarakunan Abbasiyawa guda uku, wato Haruna Rashid, da 'ya'yansa Amin da Ma'amun. Bayan mutuwar Haruna Rashid, an samu rikici tsakanin Ma'amun da dan'uwansa Amin, wanda a lokacin shi ne ya dare karagar mulki, lamarin da ya yi sanadiyyar faruwar yaki da zubar da jinin al'umma har aka kashe Amin, kana Ma'amun ya haye mulkin al'umma.
Kamar yadda dai aka sani, Abbasiyawa sun dare karagar mulkin musulmi ne ta hanyar amfani da taken kare hakkokin Ahlulbait, da haka ne ma suka sami daman kawar da masu mulkin Umayyawa. To sai dai kuma bayan samun mulkin sai suka fara juya wa Ahlulbaitin baya da kuma neman ganin bayansu ta hanyar cutar da su ta hanyoyi daban-daban, lamarin da ya haifar da wadansu yunkure-yunkure da bore daga wajen mabiya Ahlulbaiti (a.s) akan masu mulkin Abbasiyawan na wancan lokacin.
A wancan lokacin dai adadin 'yan shi'a yana da yawa, don haka duk da cewa a zahiri gudanar da mulki ba yana hannun Imamai ba ne a wadancan lokuta, to sai dai kuma mabiya Imamai din ('yan shi'a) sun kasance suna bin Imamai din wajen karbar umurni kan abubuwan da suka shafi rayuwarsu ta duniya da kuma ta lahira. Sun yi amanna da cewa halifofin musulmi na wancan lokacin ba su wuce irin sarakunan daular Romawa da sauran dauloli ba, wadanda ba abin da ya dame su in banda neman duniya da kuma zaluntar al'umma da sace musu kudade.
To hakika ko ba a fadi ba wannan babban barazana ce ga su wadannan masu mulki, wadanda suke kiran kansu a matsayin halifofin Manzon Allah (s), don haka ne suke shirya kulle-kulle wajen ganin bayan Imamai (a.s) da kuma wadannan mabiya na su.
To kamar sauran Imamai, shi ma Imam Ridha (a.s) bai tsira daga irin wadannan makirce-makirce na masu mulkin ba. Sun kasance sukan sa idanuwa a kansa da kuma kula da dukkan abin da yake yi. Muna iya takaita dalilan da ya sa masu mulkin lokacin Imam Ridha din suke yi masa hakan:
Imanin da al'umma suka yi na cewa shi ne halifan Manzon Allah (s) na hakika, sauran sarakunan kuwa 'yan fashi ne kawai wadanda suka yi fashin hakkin da ba nasu ba. Don haka ne masu mulkin suke ganinsa a matsayin wani babban abokin gaba.
Irin dabi'u da dimbin ilmin da Imam din yake da shi wanda sun kasance abubuwan da suke jawo hankulan mutane da masana zuwa gare shi, don amfanuwa da irin wadannan dabi'u da dimbin ilmin da ya gada daga wajen iyaye da kakanninsa. To shi ma wannan din ya kasance abin damuwa ga wadannan masu mulki, don ganin hakan babbar barazana ce ga kasantuwansu a kan karagar mulki da kuma burinsu na ci gaba da zaluntar mutane.
Irin yadda mutane suke ganin Imam Ridha (a.s) a matsayin mutumin da ya dace ya jagorance su, don magance musu matsaloli na siyasa da tattalin arzikin da suke ciki, saboda imanin da suke da shi na cewa babu yadda za a yi ya zalunce su matukar dai mulkinsu yana hannunsa ne. Hakan kuwa saboda irin dabi'arsa da suka gani ne na damuwa da su da kuma irin halin da suke ciki, na farin ciki ne ko kuma akasin hakan.
Baya kuma ga masu mulkin su kansu akwai kuma wasu mutane da suke ganin kasantuwan Imam din babbar barazana ce ga hanyar samun kudadensu da kuma hawa kan al'umma, daga cikin wadannan mutane kuwa malamai da sauran 'yan siyasa su ne a kan gaba. Don haka suka dau matakan kai sara da kuma sukan Imam (a.s) zuwa ga mahukuntan wancan lokacin don ganin bayansa su kuma su ci karensu babu babbaka.
Sai dai kuma yana da kyau a fahimci cewa wadannan abubuwa da muka ambata a sama, ba wai kawai sun takaita ga Imam Ridha din ba ne, face dai dukkan Imaman Ahlulbaiti (a.s) tun daga kan Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib har zuwa Imam Askari (a.s) don sun fuskanci wadannan matsaloli da muka ambata a sama.