ILMIN IMAM RIDHA (A.S):

Ilmi dai wani abu ne da aka san Mutanen Gidan Manzon Allah (s) da shi wanda babu wani wanda zai yi musun hakan ko da kuwa makiyinsu ne. Don haka Imam Ridha (a.s) a matsayinsa na daya daga cikin wadannan "Taurari Masu Haske da Haskakawa", ya gaji ilmin da wadannan iyaye da kakanninsa, ta yadda ya kasance mafi ilmi a zamaninsa wanda ya ke shayar da masu kishirwan ilmi. Tarihi dai ya nakalto mana irin dimbin ilmin da ya ke da shi da kuma yadda ya ketare dukkan masu ilmi na lokacinsa, ta yadda idan da abin a kwatanta ilminsa da ilmin sauran malaman lokacinsa, sai a ga nasu ilmin ba abin komai ya ke ba.

An ruwaito Ibrahim ibn Abbas al-Suli (daya daga cikin sahabban Imam din) yana cewa: "Ban taba ganin (Imam) al-Ridha (a.s) ya gagara amsa wata tambaya da aka gabatar masa ba, kamar yadda kuma ban taba ganin wani malamin da ya fi shi ilmi ba. Ma'amun ya kasance ya kan kira shi don gwada shi ta hanyar tambayarsa tambayoyi, inda ya kan ba shi amsa gamsassu daga cikin Alkur'ani mai girma".

Rajah ibn Abul Dahhak, wanda Ma'amun ya tura shi ya taho da Imam Ridha zuwa fadarsa ya ce: "Wallahi! Ban taba ganin wani mutum da ya fi shi (Imam Ridha) tsoron Allah da kuma zikiri a kowani lokaci ba. Mutane su kan zo wurinsa a duk lokacin da suka san ya iso garinsu suna masu tambayansa tambayoyi dangane da addininsu, shi kuwa yana mai ba su amsa ta hanyar karanto hadisai daga mahaifansa har zuwa Ali wanda shi kuma ya nakalto daga Manzon Allah (s). Lokacin da muka iso Ma'amun ya tambaye ni kan yadda ya kasance a yayin wannan tafiya ta mu, ni kuwa na gaya duk abin da na gani yayin da muke tafiya, da daddare ne ko kuma da rana, muna cikin tafiyan ne ko kuma muna tsaye, sai ya ce: "Na'am, Ya kai Dan Dahhak! Ai wannan shi ne mafi daukakan mutane a bayan kasa, mafi saninsu kana kuma mafi tsoron Allansu".

An ruwaito Ma'amun yayin da yake mai martani ga Bani Hashim a kan zaban Imam Ridha (a.s) a matsayin yarimansa mai jiran gado, yana cewa: "Dangane da mayar da martaninku kan zaben da Ma'amun ya yi wa Abul Hasan al-Ridha a matsayin magajinsa, ya kamata ku san cewa Ma'amun bai yi wannan zabe ba face sai da ya san dukkan abin da yake tattare da shi, yana mai sane da cewa a duk bayan kasa babu wani mutum guda da ya fi shi daukaka, tsoron Allah, tsantsani, wanda ya fi kowa karbuwa a wajen dukkan mutane talakawansu da masu mulkinsu kamar sa (Imam Ridha)".

Tattaunawa Da Malamai:

An ruwaito cewa wata rana Ma'amun ya yanke shawarar gayyatar malamai daga dukkan addinai don su zo su tattauna da Imam Ridha (a.s) amma fa da nufin ya kaskantar da Imam din ne don yana tunanin cewa malaman za su kure Imam.

Don haka bayan da malaman suka taru sai ya sa aka kira Imam Ridha (a.s) don su tattauna. Koda da Imam ya fito sai dukkan malaman nan suka mike tsaye don girmama shi. Lokacin da ya zauna, sai Ma'amun ya dubi "Jasaleek" babban malamin kirista ya ce masa, ya tambayi Imam Ridha (a.s) dukkan abin da yake so. Sai ya ce wa Imam: "Mene ne ra'ayinka kan Issa Almasihu?" sai Imam ya ce masa: "Mu mun yi imani cewa shi Annabin Allah ne". Sai wannan malamin Kiristan ya sake tambayarsa cewa: "Wata hujja ka ke da ita dangane da annabcin Annabinku?". Sai Imam ya ce masa: "A'a ashe ba ka karanta ba cikin Linjila cewa Yohanna ya nakalto fadin Isa (a.s) cewa; "Wani Annabi zai zo a bayana, wanda zai kasance cikamakin dukkan addinan sauran Annabawa?

Sai ya ce: "E lalle kan, to amma ai bai ambaci sunansa ba da kuma inda zai kasance ba".

Sai Imam (a.s) ya ce: "Shin kana son in gaya maka inda ya fada din cikin Linjilar?".

Sai ya ce: E, karanto min".

Sai Imam ya karanto masa ayar har inda Isa (a.s) din yake cewa: "Ni zan wuce zuwa ga Ubangiji to ammma "Barklita" wanda yake nufin "Muhammad" zai zo muku kuma zai karya da kuma lalata kafirci".

Daga nan sai wannan malamin Kirista ya yi shiru bai sake cewa komai ba.

Sai Imam (a.s) ya juya kan shugaban yahudawa ya ce masa: "Mene ne hujjarku kan annabcin Musa (a.s)?.

Sai ya ce: "Musa yana da mu'ujuzozi da suka hada da juya sanda zuwa ga maciji, tsaga kogin Nilu da kuma bi ta cikinsa da kuma hasken da ya ke fitowa a hannunsa".

Imam Ridha (a.s) ya ce masa: "To me ya sa ba ku yi imani da Isa (a.s) ba?".

Sai ya ce: "Mabiyansa suna ikirarin cewa yana tayar da macecce kana kuma yana yin maganin kuturta, to amma mu ba mu ga hakan ba ballantana mu yi imani da shi".

Sai Imam Ridha (a.s) ya ce masa: "In haka ne me ya sa kuka yi imani da sauran Annabawa? Kai hatta ma akan shi Musan, shin kun taba ganin mu'ujuzansa ne?

Sai ya ce: "Lalle haka aka gaya mana...."

Sai Imam ya ce masa: "Ta ya ya kuka san wadannan maganganu?".

Sai ya ce: "Ta hanyar tarihi da kuma wadanda suka jiyo su daga gare shi".

Sai Ima ya ce: "To ai su ma ta hanyar tarihin suke kafa hujjojinsu, shin ta ya ya za ku kira su zuwa ga addininku?".

Sai wannan bayahude ya yi shiru bai sake cewa komai ba.

Hakan nan dai aka ta yi tsakanin Imam da sauran malaman addinan har dai ya samu nasara a kansu gaba daya kuma ya kure su.

Wannan lamari dai bai yi dadi wa Ma'amun ba saboda ganin burinsa bai cika ba, don haka ya yi dan da na sanin shirya wannan taro, don kuwa maimakon mutumcin Imam ya zube sai ma kara daukaka ya yi a idon mutane baya ga wadanda suka musulunta daga cikin wadannan malamai.

Wannan kadan kenan daga cikin ilmin Imam Ridha (a.s), mai son karin bayani kuma sai ya koma zuwa ga sauran littafa don ganinsu.