YANAYIN SIYASA DA KE KEWAYE DA HAIHUWAR MAHDI :

________________________

Tarihi dai ya nakalto mana irin mawuyacin halin da Imam Hasan al-Askari (a.s) ya fuskanta daga wajen sarakunan Abbasiyawa na lokacinsa, kamar yadda kuma muka ga irin halin dar-dar da rashin zaman lafiya na siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da tsaro da al’umma suke fuskanta da kuma irin tsoron da mahukunta suke da shi cikin zukatansu dangane da Ahlulbaiti (a.s).

 A daidai wannan lokaci na dar-dar da aka haifi Imam al-Mahdi (a.s) a cikinsa ne kuma aka kashe halifan Abbasiyawa al-Mu’utaz a watan Rajab shekara ta 255 hijiriyya, wato kimanin kwanaki goma sha takwas da haihuwar Imam al-Mahdi (a.s) kenan. Bayan kashe Mu’utaz sai dansa al-Muhtadi ya dare karagar mulki da ci gaba da ayyukan da iyaye da kakanninsa suka fara.

 Bisa wannan bayani, kamar yadda kuma ruwayoyi suka kawo, an haifi Imam al-Mahdi ne a lokacin mulkin Muhammad al-Muhtadi, wanda mulkinsa ya ci gaba har na kimanin shekara guda, kafin rikici ya shiga tsakaninsa da Kurdawan lokacin inda suka kama shi da kuma kashe shi a watan Rajab shekara ta 256 hijiriyya, sai kuma al-Mu’utamid ya dare karagar mulki.

 Cikin wannan lokaci dai Ahlulbaiti da mabiyansu sun fuskanci tsananin matsin lamba, abin da ya haifar da yunkure-yunkuren mabiya Ahlulbaiti don fuskantar mahukuntan.

Abul Faraj al-Isfahani ya ambaci sunayen zuriyar Ali (a.s) da mabiya Ahlulbaitin da aka kashe ko kuma suka mutu a gidajen yarin mahukuntan saboda azaba, kamar yadda kuma ya kawo bayani kan yadda wannan zalunci na Abbasiyawa ya yadu zuwa garuruwa daban-daban. Kamar yadda kuma al-Yakubi, masanin tarihi, shi ma ya ruwaito wani sashi na irin zaluncin Abbasiyawan.

 Abu ne dai da yake a fili cewa halifofin Abbasiyawa sun riga da sun san cewa imamanci dai zai kasance a zuriyar Husaini (a.s), don haka suka takurawa Imam al-Sadik (a.s) da sauran imaman da suka zo bayansa, inda suka sanya wasunsu a gidajen yari tare da mabiyansu da kuma kashe su, don kuwa suna da masaniyar cewa imamanci dai za ta kai ga al-Mahdi al-Mau’ud dan Imam al-Askari (a.s).

 Shaikh al-Mufid(ð) ya bayyana cewa tsoron irin ta’addancin da ake wa zuriyar Ali (a.s) da kuma masaniyar da Abbasiyawa suke da shi na cewa karshen imamanci zai zo daga zuriyar Imam al-Askari (a.s) da kuma kokarin da suke yi na kawo karshen imamancin, shi ne abin da ya sanya Imam al-Askari (a.s) ya boye zance haihuwar dansa da kuma boye shi daga idon mutane. Haka nan kuma duk wani mutumin da ma yake magana kan Imam al-Mahdi ya kan fuskanci azabobi da takurawa daban daban. Ga abin da yake cewa:

 “Mabiya Abu Muhammad saboda fadin haka – wato fadin imamancin al-Mahdi – sukan fuskanci matsaloli da suka hada da tsarewa, barazana, kaskantarwa…..([1])”.

Shaikh al-Mufid dai ya rayu ne tsakanin shekara ta 338-413 hijiriyya, kusa da lokacin zamanin wakilan Imam al-Mahdi na musamman, wato lokacin Ghaibat al-Sughra (karamar buya) ta Imam al-Mahdi (a.s) wacce ta kare a shekara ta 329.



(ð). Shi ne Muhammad bn Muhammad bn al-Nu’uman al-Akbari al-Bagdadi.

([1]). Al-Irshad na Mufid, shafi na 234.