MATSAYA BAYAN SHAHADAR IMAM AL-ASKARI (A.S):
________________________
Imam al-Askari (a.s) ya yi shahada ne a
shekara ta 260 hijiriyya, wannan shahada tasa kuwa ta haifar da damuwa da rudu
mai girman gaske tsakanin ‘yan shi’a, ga tambayoyi daban-daban da suke ta
fitowa, wasu na cewa, a’a shin Imam al-Askari ba shi da dan da zai gaje shi ne?
Ko kuma shi kenan imamanci ya kawo karshe ne a bayansa don kuwa ba shi da da?
An ta samun jawabai da amsoshi dai kala-kala.
To sai dai kuma da yake
wasu daga cikin na kurkusa da shi daman sun riga da sun san cewa yana da da,
wato sun riga da sun sa zancen haihuwar Imam al-Mahdi (a.s), don haka sun amsa
wa mutane wadannan tambayoyi nasu da kuma tabbatar musu da cewa yana da da,
lamarin da ya kawar da wannan damuwa da suke da ita. A takaice an tabbatar da
cewa Imam al-Mahdi dai shi ne Muhammad bn Hasan al-Askari wanda aka
haifa cikin sirri a garin
Samarra gabannin shahadar
mahaifinsa da shekaru biyar.
Haka dai Allah Madaukakin
Sarki Ya so Ya tsawaita shekarun bayyanarsa, don ya cika duniya da adalci bayan
ta cika da zalunci.
|