AL-MAHDI (A.S) CIKIN SUNNAR ANNABI (S.A.W.A):

________________________

Littattafan ruwayoyi da hadisai sun ruwaito mana hadisai da dama da Manzon Allah (s.a.w.a) ya ke sanar da al’ummar batun al-Mahdi (a.s) da kuma cewa zai cika duniya da adalci da daidaito bayan ta cika da zalunci da babakere. Don haka za mu iya fahimtar cewa imani da kasantuwan al-Mahdi (a.s) akida ce ta Musulunci da dukkan musulmi suka yi imani da ita.

Sayyid Abdullah Shabbar cikin littafinsa Hak al-Yakin ya nakalto cewa:

“Ku sani cewa akwai busharar bayyanar Mahdi (a.s) cikin ingantattun hadisan shi’a da sunna, kuma zai kasance cikin buya. Daga cikin wadanda suka ruwaito wadannan hadisai a bangaren sunna kuwa har da, Bukhari, Muslim, Abu Dawud, Tirmizi da mawallafin Jami al-Usuli da dai sauransu. Hakika an ruwaito sama da hadisai dari da hamsin daga bangaren ‘yan sunna da suka magana kan bayyanar al-Mahdi (a.s), kamar yadda kuma an samu irin wadannan hadisai cikin karbabbun littattafa da suka dora hadisai dubu guda. Cikin littafin Al-Sawa’ik al-Muhrika na Ibn Hajr kan yanayin al-Askari (a.s) an rubuta cewa: ‘Babu wani da ya gaje shi (al-Askari) face dansa Abul Kasim Muhammadu al-Hujja (a.s), shekarunsa kuwa biyar ne yayin wafatin mahaifinsa, to sai dai kuma Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi hikima kuma ana kiransa da Al-Ka’im al-Muntazar, hakan kuwa saboda ya buya ne a Madina, ba a san inda ya je ba. Akwai wasu ma da suka ruwaito maganganu kansa daga bangaren ‘yan sunna irinsu Ibn Khalkan da mawallafan al-Fusul al-Muhimma, Madalib al-Su’al, Shawahid al-Nubuwwa da dai sauransu([1]).

Har ila yau akwai wasu hadisan kuma da suka yi magana kan bayyanar Imam al-Mahdi (a.s) da kuma siffofinsa: Bayanai kan wannan bawan Allah da kuma ishara gare su ya zo cikin wadannan ruwayoyi, don jama’a su fahimce shi da kuma tsira daga sharri masu da’awar su ne shi.

Daga cikin wadannan siffofi da ruwayoyi suka kawo akwai:

1-      Jaddadawa cewa shi Bakuraishe ne: “Ahmad da Mawardi sun ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Ku yi bushara da al-Mahdi, shi Bakuraishe ne, daga cikin zuriyata, zai bayyana a sabanin zaton mutane, zai cika duniya da adalci da daidaito kamar yadda ta cika da zalunci da babakere([2])”.

2-      Cewa Mahdi (a.s) zai kasance ne daga ‘ya’yan Abdul Mutallib: Ibn Majah ya ruwaito daga Anas bn Malik cewa: “Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Mu ‘ya’yan Abdul Mutallib mu ne shuwagabannin ‘yan aljanna, ni da Hamza da Aliyu da Ja’afar da Hasan da Husaini da Mahdi([3]).

3-      Cewa Mahdi daga Zuriyar Manzon Allah (s.) ya ke kuma sunansa Muhammadu ne: Imam Ahmad bn Hambal yana cewa: “Fadhl bn Dalin ya gaya mana, haka nan Yasin al-Ajli ya gaya mana daga Ibrahim bn Muhammadu bn al-Hanafiyya, daga babansa Aliyu cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Mahdi daga cikinmu Ahlulbaiti ya ke, Allah Zai yi gyara da shi (zai tayar da shi) cikin dare guda([4]).

Haka nan kuma ya ruwaito daga Sufyan cewa: Duniya ba za ta kare ba har sai wani mutum daga cikin mutanen gidana, wanda sunansa irin sunana ne, ya mallake ta([5]).

Ahmad bn Hambal da Abu Na’im sun fitar daga Abu Sa’id al-Khudri cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Duniya ba za ta kare ba har sai wani mutum daga zuriyata ya mallake ta, ya kuma cika duniyar da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci….”.

4-      Cewar Mahdi daga zuriyar Fatima (a.s) yake: Ibn Majah cikin Sunan dinsa ya ruwaito daga Sa’id bn al-Musayyab cewa: Mun kasance tare da Umm Salama, sai muka ambaci Mahdi, sai ta ce: Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Mahdi daga cikin zuriyar Fatima yake([6]).

5-     Cewar halifofi guda sha biyu ne([7]): Wasu ruwa-yoyin suna jaddada cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi nassi ne a kan imamai (halifofi) sha biyu, na farkonsu Aliyu bn Abi Talib (a.s) na karshensu kuwa Muhammadu al-Mahdi bn Hasan al-Askari (a.s).

Wadannan hadisai dai- da ma wasunsu – da suke magana kan cewa Mahdi zai kasance ne daga Ahlulbaiti, daga ‘ya’yan Fatima kana kuma zuriyar Imam Husain (a.s), suna bayyana mana siffofin Imam al-Mahdi (a.s) ne, musamman ma bisa la’akari da cewa wadannan hadisai ingantattu ne a bisa mahangar shi’a da sunna.

Kamar yadda kuma wadannan hadisai sun kai haddin da babu wanda yake shakku a kansu, kai hatta ma dai dukkan malaman musulmi na da da na yanzu sun tafi akan samuwar al-Mahdi al-Muntazar (a.s).

Sheikh Abdul Muhsin al-Ibad([8]), memba a kwamitin koyarwa na Jami’ar Musulunci ta birnin Madina al-Munawwara, cikin wani jawabi da ya gabatar mai suna “Akidar Ahlussunna Kan al-Mahdi al-Muntazar”, ya ambato sunayen sahabban da suka ruwaito hadisai kan Mahdi daga Manzon Allah (s.a.w.a), inda ya kawo sunayen ashirin da shida daga cikin manyan sahabbai, kamar yadda kuma ya ambato sunayen malamai talatin da takwas da suka ambato wadannan hadisai cikin littattafansu, daga cikinsu kuwa akwai Abu Dawud cikin Sunan dinsa, Tirmizi cikin Jami’i dinsa, Ibn Majah cikin Sunan dinsa, Nisa'i cikin Sunan dinsa, Ahmad bn Hambal cikin Musnad dinsa, Ibn Habban cikin sahihinsa, al-Hakim cikin Mustadrak dinsa da dai sauransu.

Haka nan Abdul’Aziz bn Baz, shugaban jami’ar Musulunci ta Madina yana cewa: “Hakika al’amarin Mahdi sanannen al’amari ne, akwai hadisai da dama (mutawatirai) da suka zo kan wannan batu, kuma a gaskiya suna nuni da cewa lalle lamarin wannan mutumin da aka yi alkawarin bayyanarsa an tabbatar da shi, kuma gaskiya ne([9])”.



([1]). Hakk al-Yakin na Abdullah al-Shabbar, shafi na 222.

([2]). Sawa’ik al-Muhrika na Ibn Hajr al-Askalani, shafi na 99.

([3]). Sunan Ibn Majah, juzu’i na 2, shafi na 1368.

([4]). Al-Jami al-Sagir na Suyuti, juzu’i na 2, shafi na 580.

([5]). Kanz al-Ummal na al-Muttaki al-Hindi, juzu’i na 14, shafi 263.

([6]). Sunan Ibn Majah, juzu’i na 2, shafi na 1368.

([7]). Jabir bn Samrata ya ce: ‘Wata rana ni da mahaifina mun je wajen Manzon Allah (s.a.w.a) inda muka ji shi yana cewa: Hakika wannan al’amari ba zai kare ba har sai an samu halifofi guda goma sha biyu”, sai ya fadi wani abin da ban ji ba, sai ya ce: sai na ce wa babana me ya ce ne: sai ya ce min: ya ce ne dukkansu Kuraishawa ne. Dubi Sahih Muslim/ Kitab al-Imarah, hadisi na 3393.

([8]). Muhadharat Haula al-Imam al-Mahdi na Abdul Muhsin al-Ibad, shafi na 26.

([9]). Mujallar Al-Jami’at al-Islamiyya, adadi na 3, shafi na 161 zuwa na162.