|
|
| |||
|
________________________
Kafin bayyanar Musulunci, dan’Adam dai
ya rayu cikin yanayi na jahiliyya mai tsanani cikin karnoni da dama, kafin daga
baya hasken Musulunci da shiriyar da Manzon Allah (s.a.w.a) yazo da ita ya
bayyana ya kuma haskaka duniya.
A wancan lokacin dai dan’Adam
yana rayuwa ne cikin yanayi na dar-dar da yanke kauna, sai dai kuma lokacin da
ya ji
Haka dai lamarin yake, a
duk lokacin da aka samu duhun jahiliyya ya mamaye duniya, al’umma suka yanke kauna
da fata, sai a samu wani sako na Ubangiji da zai zo ya yaye wannan duhu daga
)وَ إِنْ
مِنْ أُمَّةٍ إلاّ خَلاَ فِيها نَذِيرٌ( “Kuma babu wata al’umma face wani mai gargadi ya shude a
cikinta”.
(
Haka dai hasken Alkur’ani ya ratsa
duniya, ya kawar da duhun jahiliyya, ya mayar wa dan’Adam da ‘yanci da
karamarsa da azzalumai suka hana shi.
Ta hakan ne kuma
tausayawar Ubangiji ta samu dan’Adam da kuma shiryar da shi a duk zamunna.
A fili yake dai cewa
samuwar Mahdi mai gyara yana nuni ne da kulawa ta Ubangiji mai wanzuwa kana
kuma tausayawar Ubangiji wacce aka kira dan’Adam zuwa ga dakonta, kamar yadda
aka bukace shi da ya zauna cikin shirin dakon Annabawa masu kawo gyara.
Hakika duk mutumin da
yayi biris da wannan alkawari na Ubangiji na gadar da kasa da sahilan bayi,
kuma bai yi imani da bayyanar Al-Mahdi mai kawo gyara ba, babu shakka zai samu
kansa cikin yanayi na yanke kauna da rashin fata.
Kamar yadda kuma kira
zuwa ga gaskiya da Alkur’ani mai girma ya yi wa dan’Adam kana kuma Manzon Allah
(s.a.w.a) ya yi bayani kanta, ita ce kira zuwa ga aiki, jihadi da kuma kawo
gyara, a daidai lokacin da ‘yan’Adam suke jiran dakon Mai gyaran da aka yi musu
alkawarin bayyanarsa, don su share fagen mallakar duniya ga salihan bayi da
halifancin Wanda aka jima ana jiran bayyanarsa (a.s).
Tarihi ya tabbatar da
cewa al’ummomin da suka zo gabannin aiko Annabawa masu kawo gyara, sun kasance
cikin jiran dakon samuwar wani Annabi da zai kawo musu gyara cikin al’amurransu
da rayuwa cikin yalwa da tsaro, don su taru a karkashin tutar wannan aikakken
Annabi. To sai dai kuma bayan kawo karshen annabci da annabcin Manzon Allah
(s.a.w.a), Allah Madaukakin Sarki Ya kaddara cewa wannan gyara da al’umma suke
so zai kasance ne a hannun wani Imami daga zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a),
wanda zai gina wannan aiki nasa na kawo gyara ne karkashin Littafin Allah da sunnar
ManzonSa (s.a.w.a).
Don haka kula da kuma ba da muhimmanci
ga wannan lamari na Imam al-Mahdi (a.s) wajibi ne, kamar yadda kuma aiki da ba
da kokari don share fagen bayyanarsa da kuma riko da tafarkinsa shi ma wajibi
ne. Haka nan ma addu’a da kuma neman taimakon Ubangiji wajen gaggauta
bayyanarsa (a.s) shi ma dai yana da nasa gudummawar da kuma muhimmanci.
Irin wannan kauna dai na
daga cikin abubuwan da suke dada karfafa al’ummar musulmi a duk inda suke wajen
cewa nan gaba za su sake rayuwa karkashin iko na addininsu kana kuma cikin
adalci da daidaituwa ba tare da tsangwama da kawar musu da ‘yancinsu ba. Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Aba Saleh al-Mahdi ranar da aka haifeka, ranar da ka shiga buya da kuma ranar da za ka bayyana alhali jama’a suna cikin dakon jiranka don ka tabbatar da adalci a bayan kasa bayan an cika ta da zalunci da babakere. |
||||