|
|
| |||
|
________________________
An haifi
al-Mahdi (a.s) ne a daren sha biyar ga watan Sha’aban shekara ta dari biyu da hamsin
da biyar bayan hijira, mahaifinsa Imam al-Askari (a.s) ya yi shahada ne a
lokacin da Imam al-Mahdi (a.s) yake da shekaru biyar a duniya, don haka an
haifi Imam al-Mahdi (a.s) ne a lokacin halifancin al-Muhtadi al-Abbasi, wato
lokacin fitina da zaman dar-dar.
Bayan haihuwarsa dai, mahaifinsa Imam al-Askari
(a.s) ya kewaye shi da cikakkiyar kulawa saboda kare rayuwarsa da kuma cika alkawarin
Ubangiji da kuma imamancin da shi ma ya gada daga iyaye da kakanninsa. Hakan
kuwa ya biyo bayan bincikensa da azzaluman mahukuntan lokacin suke yi don kashe
shi.
Shaikh al-Saduk ya ruwaito daga Ahmad bn Hasan
bn Ishak al-Kummi cewa:
“Lokacin da aka haifi Imam al-Mahdi (a.s),
shugabanmu Abu Muhammadu al-Hasan bn Ali (al-Askari) (a.s) ya aike wa kakana
Ahmad bn Ishak da wasika da rubutunsa da kuma sa hannunsa (inda yake cewa): An
haifi jaririn, ka kiyaye wannan batu, kada ka sanar da dukkan mutane, don ba za
mu gaya wa kowa ba sai na kurkusa da masu imani wilayansa, mun sanar da kai ne
don Allah Ya faranta maka rai kamar yadda Ya faranta mana. Wassalam([1])”.
Haka nan Shaikh
al-Saduk ya ruwaito cewa Ahmad bn Ishak ya ce:
“Na ji Abu Muhammadu al-Hasan bn Ali al-Askari
(a.s) yana cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah Wanda bai dauki raina ba har
sai da na ga wanda zai gaje ni, mafi kamanci da Manzon Allah (s.a.w.a) a
halitta da aiki tsakankanin mutane, Allah Madaukakin Sarki Zai kare shi a
lokacin buyarsa, daga baya kuma ya bayyanar da shi don ya cika duniya da adalci
da daidaito bayan ta cika da zalunci da babakere([2])”.
Yayin da yake
magana
“Sai dansa, wanda ake jira don kafa daular
gaskiya ya gaje shi, kafin haka dai ya boye haihuwa da kuma al’amarinsa saboda
yanayin wancan lokacin, tsananin nemansa da shuwagabannin lokacin suke yi,
bayanan da suka watsu dangane da shi tsakanin shi’a da kuma jiran dakon da suke
masa, don haka ne mahaifinsa bai bayyanar da shi ga al’umma a lokacin rayuwarsa
ba kamar yadda kuma ba su san shi ba bayan wafatinsa([3])”.
Dukkan ruwayoyi daga bangarorin shi’a da sunna
sun tafi a
1-
Daga zuriyar
2-
Daga zuriyar Husain (a.s).
Wannan dai abu
ne da dukkan musulmi suka tabbatar da shi duk kuwa da sabanin mazhaba da
ra’ayuyyukan da suke da shi, to sai dai kuma kari
1-
Muhammadu bn al-Hasan al-Askari (a.s).
2-
Kuma shekarunsa biyar ne lokacin wafatin
mahaifinsa.
3-
Kuma, cikin ikon Allah, ya buya daga idanuwan
mutane, kuma wannan buya tasa tana da marhaloli guda biyu:
a). Marhalar Karamar Buya:
A wannan lokaci ya
b). Marhalar Babbar Buya: A
wannan lokaci saduwarsa da mutane ta hanyar wadannan wakilai ta kawo karshe
bayan ya sanar da su haka, don haka sai ya koma da su wajen malamai (al-Fukaha’)
har lokacin da zai samu yanayin da ya dace don bayyanarsa da kuma gyaran
al’umma da tsayar da daular adalci ta Ubangiji da aka jima ana jiranta.
Hakika Manzon Allah
(s.a.w.a) a ruwayoyi da dama ya bayyana matsayin Ahlulbaiti (a.s) da kuma
wajibcin binsu da riko da tafarkinsu, daga cikinsu kuwa har da fadinsa
(s.a.w.a) cewa: “Matsayin Ahlulbaitina a cikinku kamar matsayin Jirgin
(Annabi) Nuhu ne, wanda ya hau shi ya tsira, wanda kuwa ya saba masa ya
halaka”.
Da kuma fadinsa (s.a.w.a)
cewa: “Lalle ni na bar muku wasu nauyaya guda biyu: Littafin Allah da
Zuriyata Ahlulbaiti, matukar kuka yi riko da su to ba za ku taba bata ba([4])”.
Har ila yau kuma a cikin wadannan
ruwayoyi akwai ishara ga ci gaban kasantuwan Ahlulbaiti (a.s) a gefen Alkur’ani
mai girma, wato Alkur’ani da Ahlulbaiti ba za su taba rabuwa ba. Bugu da kari
kuma akwai wasu hadisan daga Manzon Allah (s.a.w.a) da suke magana kan cewa
halifofi dai guda goma sha biyu ne kuma Mahdi daga zuriyar Husaini (a.s) yake,
kamar yadda kuma akwai ruwayoyi daga Imamai (a.s) da suke nuni da cewa shi ne
na tara daga cikin ‘ya’yan Husaini, da dai sauransu da suke bayyana mana cewa
Imam al-Mahdi dai shi ne Muhammadu bn al-Hasan al-Askari (a.s).
Ala kulli halin dai, dukkan musulmi dai sun tafi a kan
imani da Mahdi (a.s) da kuma cewa shi ne mai gyara da kuma ‘yantar da wannan
al’umma daga zaluncin da take ciki.
|
||||