|
|
| |||
|
________________________
Rikici tsakanin alheri da sharri a doron kasa dai ya faro ne
tun daga farko-farkon wannan duniya tamu, kuma wannan gasa da rikici zai ci
gaba da samuwa tsakanin tafarkoki guda biyu; tafarkin shiriya da tafarkin bata;
tafarkin Annabawa da tafarkin jahilai dawagitai.
Hakika
sakon Musulunci ya samu nasara ta hannun Manzon Allah (s.a.w.a) kuma haka
wannan tafarki ya ci gaba har ya gina tafarkin tauhidi, ya ciyar da dan’Adam
gaba bisa asasin ilmi da imani, ya samu haskakuwa da wannan haske kana kuma ya
shiryu da wannan shiriya madaukakiya.
To
sai dai kuma daga baya wannan tafarki ya fara yin rauni, lokacin da wasu akidu
da wayewa na jahiliyya suka fara kunno kai, aka fara samun koma baya a wayewa
ta Musulunci, aka hana dan’Adam rayuwa karkashin inuwar imani, gaskiya, adalci
da zaman lafiya. A bangare guda kuma zalunci ya ci gaba da yaduwa a fadin
duniya, al’adun jahiliyya suka fara samun gindin zama, har muminai suka fara
yanke kauna, ba don dai suna tunanin alkawarin Ubangiji ba na cewa zai taimaki
addininSa da kuma tabbatar da adalci da kawo karshen zalunci da fasadi ba ta
hannu wani mai kawo gyara, wanda zai tsayar da sunnar Annabawa da kuma gina
rayuwa bisa asasin Alkur’ani da Sunna Manzon Allah (s.a.w.a), wannan mutumi
kuwa shi ne ‘Mahdi (Mai Shiryarwar) wannan al’umma’ kamar yadda Manzon Allah
(s.a.w.a) ya ambace shi cikin ruwayoyi daban-daban. Babu shakka hakan kuwa alkawarin
Ubangiji ne tabbatacce cikin Alkur’ani da sauran Saukakkun litattafa.
Wannan Mai kawo gyara
dai da dawo da kaunar da muminai suke da shi na kawo karshen jahiliyya, zai
cika duniya da adalci da daidaituwa bayan ta cika da zalunci da babakere. |
||||