|
|
| |||
|
________________________
Babu shakka
bayyanar Mahdi mai kawo gyara, na daga cikin manyan abubuwan da za su faru a
tarihin dan’Adam, don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya sanar da al’ummarsa
abin da Allah Madaukakin Sarki ya sanar da shi na bayyanar wannan mai babban
mai kawo gyara. Hakika Manzon Allah (s.a.w.a) ya nusar da al’ummarsa kan wannan
lamari da kuma umurtansu da su yi imani da shi da kuma binsa a lokacin
bayyanarsa a matsayin mai kawo gyara, wanda zai yi aiki da littafin Allah da
sunnar ManzonSa (s.a.w.a), wanda kuma zai jagoranci al’umma zuwa ga tafarkin
shiriya da aminci, ya ruguza gumakan jahiliyya da kuma karkatattun ra’ayuyyuka.
Don
kusato da wannan akida ta buya kusa da hankulan mutane, Manzon Allah (s.a.w.a)
da Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun yi ishara da wasu alamu na bayyana, wadanda za
su yi nuni da kusatowan wannan lokaci.
To
sai dai kuma yana da kyau a fahimci cewa makiya sun yi kokarin sanya ruwayoyi
na karya cikin ruwayoyi na hakika da suka yi magana
Ruwayoyin
da suka yi ishara da batun bayyanarsa (a.s) sun yi ishara da nau’oi guda biyu
na bayyana, wato: Alamomi na zamantakewa da kuma alamomi na dabi’a.
Alamomi na zamantakewa dai sun hadu ne a
1-
Yaduwar zalunci da babakere.
2- Samun ikon jahiliyya da kuma bayyanar dabi'u na
jahiliyya da kuma akidojinta.
3- Ci gaban ilmi mai girman gaske.
4- Faruwar yake-yake da fitinu kala-kala bugu da kari
rashin aminci da zaman lafiya.
5- Bayyanar makaryata, masu da’awar kawo gyara.
6- Tsadan kayayyaki da lalacewar tattalin arziki.
7- Bayyanar
masu sadaukarwa da ba da kawukansu wajen jagorantar kungiyoyin kawo gyara. |
||||