|
|
| |||
|
________________________
A bangaren siyasa dai wannan zamani ya kasance zamani ne mai cike da duhu a rayuwa da zamantakewa ta al'umma, hakan kuwa saboda yaduwar ayyukan ta'addanci, kisan gilla daga zato ko shakka a kan mutum, ta yadda sanya
mutum cikin kurkuku, azabtarwa da kisan gilla sun zama ruwan dare gama duniya.
A bangare guda kuma ga yaduwar fasadi, gidajen sarakuna, hakimai da makusantansu sun cika da dukiyoyin al'umma da kayayyakin kide-kide da wargi, ga kuma mawaka da ake basu makudan kudade don su rera
waka da burge sarakuna.
Ba abin da sarakuna suke yi in ban da tara gwala-gwalai, tufafin alfahari, kayayyakin wasa da wargi, gina manyan fadoji, alhali kuwa suna takurawa al'umma da sanya su cikin mummunan hali na talauci da
rashi sakamakon kwace musu kudade da suke yi, bugu da kari kan sanya su cikin gidajen yari da shan jininsu matukar dai suka nuna rashin amincewarsu(1)".
Abbasiyawa a wancan lokacin sun takurawa zuriyar Imam Ali bn Abi Talib (a.s) da mabiyansu saboda nuna rashin amincewar da suke yi wa ayyukan zalunci da kokarin lalata addini ta hanyar binsu a duk inda
suke da kwace musu dukiya da dai sauran nau'oi na zalunci saboda kar su ba su damar jagorantar duk wani yunkurin kawar da su, don kuwa sun san cewa suna da matsayi mai girma a wajen al'umma.
Duk da cewa dai yanayi na siyasa da Imam Kazim (a.s) ya ke ciki ya kasance mai wahalan gaske, takura masa da ake yi nesa ba kusa ba yafi na mahaifinsa Imam Sadik (a.s), har ila yau duk da sanya masa
ido da ake yi da kuma sanya shi cikin kurkuku da wajajen tsare mutane, to sai dai duk da haka bai bar aikata wajibin da ya hau kansa ba da kuma gudummawar da ya kamata ya bayar. Ya samu nasarar tarbiyyantar da malamai
da maruwaita hadisai, sannan kuma ya samu dakatar da batan da wasu batattun kungiyoyi na akida da falsafa suke yadawa. Malaman tarihin sun ruwaito cewa wasu daga cikin malamai, sahabbai da dalibansa sukan sadu da shi
a sirrance a cikin kurkuku don tambayansa tambayoyi kan mas'aloli daban-daban da hukumce-hukumce, shi kuma ya amsa musu wadannan bukatu nasu.
Rayuwar Imam Kazim (a.s) dai ta kasance wata marhala ta siyasa da tarihi cikin tarihin Musulunci, don kuwa Imam (a.s) ya dau nauyin imamanci ne tun daga shekara ta 148 har zuwa shekara ta 183, da ya
hada da lokacin mulkin al-Mansur, al-Mahdi, al-Hadi da Haruna Rashid, wanda shi ne lokaci mafi muni na mulkin Abbasiyawa.
A lokacin mulkin Abu Ja'afar al-Mansur Ahlulbaiti (a.s) da mabiyansu sun fuskanci mummunan yanayi na zalunci, kisa da ta'addanci.
An ruwaito cewa a lokacin, Al-Mansur ya kwace dukiyoyinsu da sanya su cikin gidajen kurkuku da wajajen tsare mutane, ya zubar da jininsu ta hanyoyi daban-daban na kisa, a wasu lokuta ma ya kan gina
tubula a kansu alhali suna raye, kamar yadda kuma ya kan hana musu abinci da abin sha, ta haka ya samu damar kashe da dama daga cikinsu cikin yunwa da kishirwa a cikin gidajen yarinsa masu duhun gaske ko kuma ta hanyar
dukansu da karafa har sai sun mutu.
Bayan mutuwar al-Mansur, dansa al-Mahdi - wanda shi ne ya dare karagar mulki - ya fara tunanin saukaka wa al'umma irin wahalhalun da suka shiga lokacin mahaifinsa, don haka sai ya sako mutanen da aka tsare
da kuma mayar musu da kudadensu da aka kwace. Wannan kuduri nasa kuwa ya hada har da Ahlulbaiti da mabiyansu, ciki kuwa har da Imam al-Kazim (a.s), wanda aka mayar masa da dukiyarsa da aka kwace.
To sai dai ba a jima ba sai al-Mahdi ya fara damuwa da irin tasirin da Imam Kazim (a.s) yake da shi a zukatan al'umma, don haka sai ya bukaci gwamnansa na garin Madina da ya turo masa da Imam (a.s).
Lokacin da Imam Kazim (a.s) ya iso garin Bagadada, sai ya yi umarnin da a sanya shi a gidan kurkuku, to amma faruwar wani lamari da ke nuni da karamar Imam (a.s) ya sa al-Mahdi ya canza wannan matsaya tasa,
inda ya yi umarni da a sake shi.
Abin da ya faru kuwa shi ne wata rana ne ya ga Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (a.s) cikin mafarkinsa yana ce masa: "Ya Muhammadu! Yaushe kuka zama haka, idan kun hau mulki ku yi fasadi a bayan
kasa kuma ku yanke zumunta(2)".
Nan take al-Mahdi ya farka a firgice, daga nan sai ya yi umarnin da a sake Imam (a.s)(3).
Ta haka ne Imam (a.s) ya koma garin Madina da ci gaba da rayuwarsa ta shiryar da mutane akan tafarkin Manzon Allah (s.a.w.a).
Bayan darewarsa karagar mulki, Musa al-Hadi ya ci gaba da siyasar da iyaye da kakanninsa suka mutu a kai na kiyayya da Ahlulbaiti da mabiyansu da takura musu rayuwa, lamarin da ya sanya mabiya Ahlulbaitin
suka kaddamar da wani yunkuri na kawar da shi karkashin jagorancin Hasan bn Ali bn Hasan bn Hasan bn Ali bn Abi Talib, ma'abucin waki'ar Fakh shekara ta 169 hijiriyya. To sai dai kuma Abbasiyawan sun fito da dukkan karfinsu wajen fuskantar masu wannan bore, inda al-Hadi din ya yi umarnin kashe dukkan wadanda aka kama da kuma ruguza gidaje da kona gonakinsu.
Ana iya cewa wannan yunkuri dai na daga cikin fitattun yunkurin da Ahlulbaiti suka yi bayan yunkurin Karbala karkashin jagorancin jikan Manzo, Husain (a.s).
Bayan kawo karshen wannan yunkuri, al-Hadi ya kuduri aniyar dirka kan Imam (a.s) da kuma sanya shi cikin kurkuku, to sai dai kuma Allah ya kawo karshensa kafin ya aikata wannan mummunan aiki nasa, inda ya mutu kana dan'uwansa Haruna Rashid ya dare karagar mulki.
|
||||