|
|
| |||
|
________________________
Kamar yadda aka sani, Imam Kazim (a.s) ya rayu da halifofin Abbasiya kamar yadda muka ganin a bangaren da muka yi bayani kan yanayin siyasa a lokacinsa da kuma irin halifofin da ya rayu da su, inda suka ci gaba da kuntata masa da sanya
shi cikin gidajen yari daban-daban har lokacin mulkin Haruna Rashid.
Haka Imam Musa al-Kazim (a.s) ya rayu cikin wannan mulki na Abbasiyawa kamar yadda sauran iyalan gidan Manzo da mabiyansu suka rayu cikin kunci, zalunci, ta'addanci, shiga gidan yari da kisan gilla.
Malaman tarihi dai sun ruwaito kadan daga cikin irin yadda gidajen yarin suke da kuma irin danyen aikin da zaluncin da ake wa Ahlulbaiti (a.s) da mabiyansu a cikinsu, musamman ma dai Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s) da mabiyansa.
A shekara ta 179 hijiriyya lokacin da Haruna Rashid ya tafi aikin hajji, sai ya yi umarnin da a kame Imam Kazim (a.s) da tura shi zuwa ga gwamnan garin Basra Isa bn Ja'afar bn al-Mansur, inda ya sanya shi cikin gidan yari har
na tsawon shekara guda, daga nan sai aka tura shi zuwa Bagadada, inda aka tsare shi a wajen Fadhl bn Rabi' na tsawon lokaci, daga nan kuma aka tsare shi a wajen al-Sindi bn Shahak.
Matukar dai muna son fahimtar irin mummunan halin da al'umma suka shiga cikin lokacin Haruna Rashid musamman ma dai Imam Kazim (a.s), to dole ne mu koma ga littafan tarihi don su hakaito mana wannan mummunan yanayi na zalunci.
A matsayin misali, tarihi ya bayyana cewa Haruna Rashid ya yi umarnin da a tube tufafin Fadhl bn Yahya al-Barmaki, daya daga cikin na kurkusa da shi, a yi ta masa bulala da ci masa mutumci a gaban al'umma don kawai ya saukaka wa
Imam da raga masa daga irin azabar da ake masa a gidan yari(1).
Har ila yau tarihi ya bayyana cewa mutanen birnin Bagadada sun shiga cikin halin damuwa da tsoro lokacin da Yahya bn Khalid al-Barkali ya iso birnin a kokarin da yake yi na shirin kashe Imam Kazim (a.s)(2).
Kamar yadda tarihi ya bayyana mana bayanan da Hamid bn Kutbah ya yi na irin zaluncin da suka aikata bayan da aka dora masa nauyin aikata ayyukan zalunci da ta'addanci a kan mabiya Ahlulbaiti da ake tsare da su a gidan yari.
Hamid ya bayyana yadda ya dauki takobi ya nufi wani gida da ke da rijiya a tsakiyansa, a cikin gidan akwai wasu dakuna da aka gina cikin kasa don tsare mutane da umarnin Haruna Rashid. Lokacin da ya shigo sai daya daga cikin bayin
Rashid ya bude masa kofa ya shigar da shi daya daga cikin wadannan dakuna inda ake tsare da mutane ashirin daga cikin zuriyar Ali bn Abi Talib da Fatima al-Zahra, 'yar Manzon Allah (s.a.w.a) da suka hada da samaruka da dattijai daure cikin sarka da
igiyoyi, daga nan sai wannan bawa ya umarce shi da ya kashe su da jefa su cikin wannan rijiya. Haka ya aikata da mutanen da suke cikin daki na biyu da na uku, har sai da ya kashe zuriyar Ali su sittin(3).
Har ila yau an ruwaito cewa Haruna Rashid ya tsare Muhammadu bn Abi Umair al-Azdi, daya daga cikin sahabban Imam Kazim (a.s) har na tsawon shekaru goma sha bakwai, alhali kuwa yana daga cikin mutanen da suka fi tsantsaini da tsoron Allah.
An azabtar da shi azaba mai tsanani, al-Kasshi ya ruwaito cewa an masa bulala har sau dari da ashirin.
Kamar yadda kuma aka ruwaito cewa 'Haruna Rashid ya tsare wasu daga cikin sahabban Imam Kazim (a.s) da suka hada da Aliyu bn Hashim bn al-Barid da Abdullah bn Alkamah da kuma Makhul bn Ibrahim al-Suhdi, a cikin daya daga cikin
gidajen yarinsa har na tsawon shekaru goma sha biyu(4).
Wannan dai kadan kenan daga cikin irin zaluncin da tarihi ya tabbatar mana da su wadanda Haruna Rashid ya aikata a lokacin mulkinsa.
|
||||