Rayuwar Imam Kazim (a.s) a Gidan Kurkuku:

________________________

Imam Kazim (a.s) dai ya riki gidan yari a matsayin masallaci, haka nan kuma wannan kadaitaka a matsayin I'itikafi da neman kusanci da Allah Madaukakin Sarki ta hanyar zikiri da sauran ibadu, ranansa kuwa ya kan cika ta ne da azumi darensa kuwa lokacin ganawa da Ubangiji da tsayuwa.

An ruwaito daya daga cikin mutanen da aka dora musu nauyin kula da Imam (a.s) a gidan yarin Isa bn Ja'afar a Basra yana cewa ya ji shi yana cewa:

"Ya Allah! Ka san cewa ina rokonka da ka kebance ni daga bayinka, ga shi kuma yanzu Ka yi hakan, dukkan godiya ta tabbata a gare Ka".

Haka nan an ruwaito cewa lokacin da Haruna Rashid ya mika Imam Kazim (a.s) ga Fadhl bn Yahya don sanya shi cikin gidan yari da azabtar da shi, an gano shi yana raya dare dukkansa da salla, karatun Alkur'ani, azumtan kusan dukkan ranaku, dukkan lokaci yana cikin ibada(1).

Haka nan kuma an ruwaito cewa Haruna Rashid ya kan dauki Imam daga wannan gidan yarin zuwa wancan, watakila don boye shaksiyyar Imam da kuma kawo karshen ruhin yunkurin kawar da shi daga zukatan al'umma saboda mantawa da Imam da za su yi kamar yadda ya ke zato.

Ganin cewa dukkan irin wadannan matakai da yake dauka ba su haifar da sakamakon da yake so ba, Haruna Rashid ya kirkiro wani tafarkin kuma na raunana ruhin Imam, hakan kuwa ta hanyar tura masa wani mutum ne da sunan neman gafarar Haruna Rashid kan abubuwan da ya yi wa Imam din da kuma neman ya sako shi, to amma Imam ya ki amincewa da hakan, yana mai amsa masa da cewa: "Gobe kiyama za ka sani idan aka tsayar da kai a gaban Allah a matsayin azzalumi mai wuce gona da iri a kan mutane. Wassalam(2).

Ta haka ne dai Imam (a.s) ya ruguza hanyoyin zalunci da babakeren Haruna Rashid da kuma irin matsin lambar da yake masa da kokarin rage tasirin da yake da shi a zukatan al'umma. To sai dai bayan da Haruna Rashid ya ga cewa ya gagara cimma abin da yake son cimmawa, sai ya ga babu abin da ya rage masa in ban da daukan mataki na karshe, wato kashe Imam (a.s) da kawo karshen rayuwarsa madaukakiya.




____________
1- A'alam al-Warah bi A'alam al-Hudah na Tabrisi, shafi na 311.

2- Bihar al-Anwar na Majlisi, juzu'i na 48, shafi na 231.