Lokacin Imam Kazim (a.s) lokaci ne da ke cike da kungiyoyi da mazhabobi na fikihu, akida da falsafa, ga kuma mazhabobi na tafsiri da hadisai, don haka wannan zamanin ya kasance daga cikin zamunna mafiya hatsari
saboda yaduwar kungiyoyin bata da yaduwar muggan akidu.
A wannan lokacin, wasu malumman fikihu da alkalan hukuma sun kasance su kan kirkiro hukumce-hukumcen da za su yi daidai da ra'ayuyyukan mahukuntan, don haka a lokacin an kirkiro hadisan karya
da kuma lalata na gaskiya, lamarin da ya kasance babbar barazana ga akidu da shari'ar Musulunci.
To sai dai duk da irin wannan lalacewa na yanayin siyasa da kuma takurawa Imam Musa al-Kazim (a.s) da mahukunta suke yi, amma dai Imam din bai bar gudanar da aikin da ya hau kansa ba da kuma
gyara irin barnar da aka yi wa akidun Musulunci. Imam Kazim (a.s) da dalibansa sun zage damtse wajen fuskantar wadannan batattun akidu, kamar yadda mahaifinsa al-Sadik (a.s) da kakansa al-Bakir (a.s) suka yi gabanninsa don tabbatar da rukunan tauhidi da tsarkake akida.
Dubi cikin taskar da Imam al-Kazim (a.s) ya bar mana zai tabbatar mana da irin muhimmancin da yake bai wa lamarin kare akidar tauhidi da kare ta daga shirka da fasadi. Kamar yadda kuma za mu ga cewa yana da tunani na samar da ilmummuka na addinin
Musulunci da kuma tafarkin tarbiyya na gina musulmin kirki.
Littattafan maruwaita hadisi da na tarihinsu sun tabbatar da cewa sama da maruwaita dari uku ne suka ruwatito hadisi daga Imam al-Kazim (a.s), kamar yadda kuma almajiransa sun taka gagarumar rawa wajen yada ilmi da wayar da kan al'umma.
____________