|
|
| |||
|
________________________
An haifi Imam Musa al-Kazim (a.s) ne a ranar Lahadi 7 ga watan Safar shekata ta 128 hijiriyya a garin Abwa da ke tsakanin Makka da Madina inda mahaifiyar Manzon Allah (s.a.w.a) Amina ta rasu kuma aka bisne ta.
Imam Musa al-Kazim (a.s) dai ya rayu ne karkashin kulawan mahaifinsa Imam Ja'afar al-Sadik (a.s), inda ya sha daga ilminsa sannan kuma ya gaji irin kyawawan dabi'unsa. Ya kasance kyawawan misalai
na kyawawan dabi'u, karimci, gudun duniya, hakuri, jaruntaka, fuskantar azzaluman mahukunta da dai sauran kyawawan halaye. A lokacin da yake raye da mahaifinsa, rayuwarsa ta kasance rayuwa ce ta tarbiyya, girma
da kuma koyo, bayansa kuwa sai ta zamanto rayuwa ce ta ci gaba da tafarkin Ahlulbaiti (a.s), tafarkin tsira kuma mai haske da haskakawa.
Kafin shahadarsa, Imam Sadik (a.s) ya yi wasicci kan imamancin dansa Imam Musa al-Kazim (a.s) a bayansa ta hanyoyi daban-daban.
Ali bn Ja'afar -dan'uwan Imam Kazim - ya ruwaito daga tabbatattun maruwaita cewa: Na ji Abu Ja'afar bn Muhammadu (a.s) yana ce ma wasu na kurkusa da shi daga cikin sahabbansa cewa: "Ku aikata
alheri ga wannan da nawa Musa don kuwa shi ne mafi daukakan 'ya'yayena, shi ne wanda zan bari bayana, shi ne zai kasance a matsayina sannan kuma hujjar Allah a kan dukkan halittu a bayana(1)".
|
||||