Dabi'un Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s):

________________________

Irin karfin halin da Imam Musa bn Ja'afar (a.s) yake da shi da kuma siffofi da zatinsa madaukaka ne ya sa ake masa lakabi da al-Abd al-Salih (Salihin Bawa) da kuma Zainul Mujtahidin (Adon Mujtahidai), saboda yawan ibada da kokarinsa, da kuma al-Kazim (Mai Kamewa) saboda yawan juriya da hakurinsa kan cutarwa da kuma mayar da cuta da kyakkyawa, da kuma Babul Hawa'ij (Kofar Bukatu) saboda haiba da matsayin da yake da shi wajen Allah da biyan bukatun mutane ta hanyar jingina da Allah Madaukakin Sarki.

Hakika sanin Allah da komawa ta gaba daya gare Shi da Ahlulbaiti (a.s) suke da shi, shi ne sirrin girma da daukakan da suke da shi sama da sauran jama'a, hakan kuwa shi ne abin da ake kira da Kamal al-Mutlak, wato Cikakkiyar Kamala.

Don haka ba abin mamaki ba ne idan har aka ga gudun abin duniya, sadaukar da kai da dukiya a tafarkin Ubangiji da neman yardarSa, bugu da kari kan ba da himma wajen 'yanto al'umma da sanya ta kan tafarkin shiriya da tsira cikin tarihin rayuwar Ahlulbaiti (a.s).

Babu shakka rayuwar Imam Kazim (a.s) madaukakiya ta kasance misdaki na wadannan abubuwa da muka ambata, don haka ga wasu ruwayoyi da suke tabbatar da haka:

"(Imam Kazim) ya kasance wanda ya fi kowa haddan Alkur'ani mai girma da karanta shi da murya mai kyau, idan yana karatun Alkur'ani mutane sukan fashe da kuka, mutanen Madina sukan kira shi da Zainul Mujtahidin(1)".

An ruwaito cewa saboda tsananin alakarsa da Ubangiji da kaunar da yake maSa da kuma neman yardarSa, Imam Kazim (a.s) ya tafi aikin hajji zuwa Dakin Allah da kafafunsa. An ce ya je aikin hajji har sau hudu da kafa tare da dan'uwansa Aliyu bn Ja'afar. Tafiyarsa ta farko ta kwashe kwanaki 26, ta biyu kuma kwanaki 25, ta uku kwanaki 24 sannan na hudu kuma kwanaki 21.

Idan kuwa ya tsaya don yin salla, idanuwansa sukan ciko da hawaye, ya kasance mai yawan neman gafara da godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Hisham bn Ahmar yana cewa: 'Wata rana na kasance tare da Abul Hasan al-Kazim muna tafiya cikin lunguna garin Madina, kwatsam sai ya sauko daga abin hawansa ya yi sujada mai tsawon gaske, daga nan sai ya dago kai ya hau abin hawan tasa, sai na ce masa: In kasance fansa gare ka, wannan sujada taka ta yi tsawo, sai ya ce: "Na tuna da wata ni'imar da Allah ya yi min ne, shi ya sa na gode wa Ubangijina(2)".

Shaikh al-Mufid yana cewa: "Ya kasance ya kanyi kuka don tsoron Allah ta yadda har gemunsa ya kan jika da hawaye, ya kasance mai sada zumunci tsakanin dangi da mutanensa, ya kasance ya kan ciyar da mabukatan mutanen Madina, cikin dare ya kan dauki abinci yana bi yana raba wa talakawa ba tare da sun san wa yake kawo musu ba(3).

An ruwaito cewa lokacin da Haruna Rashid ya daure Imam Kazim (a.s) a daya daga cikin gidajen yarinsa, shugaban gidan yarin ya ji Imam (a.s) yana cewa: "Ya Allah! Ka san cewa ina rokonka da ka kebance ni daga bayinka, ga shi kuma yanzu Ka yi hakan, dukkan godiya ta tabbata a gare Ka(4)

Haka dai halayensa suka kasance dangane da mutane ta yadda har Shaikh al-Mufid ya ke cewa: "Abul Hasan al-Kazim ya kasance mafi ibadan mutanen zamaninsa, wanda ya fi su ilmi da daukaka.

Malaman tarihi sun ruwaito cewa Imam (a.s) ya kan saka wa duk mutumin da ya cutar da shi da alheri, irin wadannan dabi'u nasa dai sun yi tasirin gaske akan al'umma da kuma janyo su zuwa tafarkinsa.

Har ila yau kuma daga cikin abubuwan da aka san shi da su, shi ne sayen bayi da 'yantar da su saboda Allah Madaukakin Sarki. Litattafan tarihi sun ruwaito kadan daga cikin irin wadannan halaye, ta yadda a wasu lokuta ya kan sayi dukkan iyali da 'yantar da su don neman yardar Allah.






____________
1- A'alam al-Warah bi A'alam al-huda na Tabari, shafi na 298.

2- Al-Kafi na Kulayni, juzu'i na 2, shafi na 98.

3- Al-Irshad na Shaikh al-Mufid, shafi na 296.

4- Bihar al-Anwar na Majlisi, juzu'i na 48, shafi na 107.