|
|
| |||
|
________________________
Zamanin Imam al-Jawad (a.s) - wanda ya kasance lokaci ne na sarakunan Abbasiyawa wato Ma'amun da Mu'utasim - ya kasance zamani ne da ta'addanci da takurawan Abbasiyawa - a zahiri - ya ragu sosai idan aka kwatanta shi da lokutan da suka gabata, duk da cewa tafarkin Abbasiyawa dai guda ne kuma yana ci gaba.
A wannan lokaci Ma'amun ya yi kokarin daga wasu take da nufin rudin mabiya Ahlulbaiti (a.s) da kawo karshen irin barazanar da yake fuskanta daga wajensu, to sai dai kuma duk da haka bai tsira daga wasu yunkure-yunkure daga mabiya Ahlulbaitin ba.
Duk da cewa a wannan lokacin Abbasiyawan sun canza siyasarsu ta zalunci, to sai dai kuma hakan bai jima sosai ba, inda suka koma kan wannan tsohuwar siyasa ta su ta tursasawa da kuma amfani da karfi a kan zuriyar Manzon Allah (s.a.w.a).
Dubi cikin ayyukan siyasa (wasiku da maganganu) da suke fitowa daga Imam al-Jawad (a.s) da kuma irin matsayar mahukunta dangane da Imam bugu da kari kan darussa da kuma karin bayani kansu, za su iya tabbatar mana da cewa Imam al-Jawad (a.s) yana gudanar da ayyukansa ne a boye saboda matsayin
da yake da shi mai zurfi cikin zukatan al'umma.
Littattafan tarihi da na hadisi sun rubuto mana wasu daga cikin irin wasikun da Imam Muhammadu al-Jawad (a.s) ya aika wa sahabbai, mabiya da wakilansa wadanda suke nuni da irin ayyukansa na boye tare da sahabbansa da suka kasance tare da shi.
Mahukuntan Abbasiyawa dai sun yi ta kokarin ganin sun toshe wadannan ayyuka na Imam (a.s) ta hanyoyi daban-daban, to sai dai kuma duk da haka Imam al-Jawad da mabiyansa sun ci gaba da gudanar da ayyukansu na shiryar da mutane da kautar da su daga karkacacciyar hanya da mahukuntan suke
kokarin dora al'umma a kai.
Hakika dubi da idon basira cikin matsayar halifofin Abbasiyawa guda biyu wato Ma'amun da Mu'atasim a kan Imam Jawad (a.s) zai tabbatar mana da irin muhim-manci da matsayin da Imam (a.s) din ya ke da shi na jagoranci cikin zukatan al'umma saboda kasantuwarsa babbar alama da ke nuni da
imamancin Ahlulbaiti (a.s) a wancan lokacin.
Irin wannan lamari ne ya sanya Ma'amun ya kira Imam al-Jawad (a.s) daga Madina a shekara ta 211 hijiriyya da kuma aurar masa da 'yarsa Umm al-Fadhl da kuma jure wa irin ka-ce-na-cen da ya shiga tsakaninsa da baffanninsa Abbasiyawa kan wannan aure. Duk da cewa dai hakan kokari ne kawai na toshe
bakin Imam din da mabiyansa da kuma janyo hankulan mutane zuwa gare shi (Ma'amun) don cimma manufofinsa na siyasa.
To sai dai tuni Imam ya fahimci wannan makirci, don haka sai ya ki amincewa da ci gaba da zama a Bagadada don ya samu tsira daga sanya idon hukuma da kuma dora masa takunkumi. Ya fifita ya koma garin Madinan Manzo don ci gaba da ayyukansa da cimma manufofinsa na jagoranci da shiryar da al'umma.
Bayan mutuwar Ma'amun dai sai al-Mu'utasim ya dare karagar mulki, to sai dai shi ma kamar iyaye da kakanninsa ya kasance mai tsananin tsoron irin matsayi na ilmi da siyasa da Ahlulbaiti (a.s) suke da shi a zukatan al'umma. Don haka sai ya kira Imam al-Jawad (a.s) daga Madina zuwa Bagadada a shekara
ta 219 hijiriyya don dusar da tauraruwarsa da kuma tasirin da yake da shi, don kuma ya kasance kusa da fadan mulki da sanya ido kansa bugu da kari kan hana shi gudanar da ayyukan ilmi da na siyasa da yake gudanarwa.
Malaman tarihi dai sun tabbatar da cewa Imam al-Jawad (a.s) bai jima a garin Bagadada ba bayan barinsa Madina, don kuwa da man Mu'atasim ya kuduri aniyar ganin bayansa ne don haka ne ma ya kira zuwa Bagadadan. Hakan kuwa ya faru, don ya sanya masa guba cikin abinci inda ya yi shahada a shekara ta
220 hijiriyya. Kamar yadda Ibn Babuwaihi ya ke cewa: "Mu'utasim ne ya sanya guba wa (Imam) Muhammadu bn Ali al-Jawad(1).
Bayan wadannan 'yan shekaru da suke cike da biyayya ga Ubangiji da kuma shiryar da al'umma na tsawon shekaru kimanin ashirin da biyar, Imam al-Jawad ya koma ga Mahaliccinsa ne a ranar shida da watan Zil Hajji shekara ta 220 hijiriyya a garin Bagadada inda aka bisne shi tare da kakansa
Imam Musa al-Kazim (a.s).
Amincin Allah Ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, ranar da ya yi shahada da ranar da za a tashe shi rayayye wanda aka zalunta.
|
||||