Matsayin Ilmin Imam Muhammad bn Ali Al-Jawad (a.s):

________________________

Kowani guda daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s) ya kasance birni ne na ilmi, Imam Jawad (a.s) ma haka ya kasance. Kamar yadda muka gani a yayin da muke bayani kan Imamancinsa na irin tattaunawar da suka yi da malamai da dai sauransu ya ishe mu shaida kan irin dimbin ilmin da yake da shi, to amma duk da haka bari mu dan yi dubi kadan cikin ilmin nasa da kuma yadda ya yada shi zuwa ga jama'a.

Imam al-Jawad (a.s), tsawon lokacin imamancinsa na kimamin shekaru 17 dai, ya ba da muhimmiyar gudummawa wajen wadatar da makarantar Ahlulbaiti da ilmi da kuma kiyaye abubuwan da suka bari wadanda suka dogara a kan nassi da hadisan Manzon Allah (s.a.w.a), fahimta kuma ciro hukumci daga Alkur'ani da sunna, bugu da kari kan muhimmancin da suke ba wa ilmi da hankali.

Imam al-Jawad (a.s) - kamar mahaifansa - ya dogara ne a kan wasu hanyoyi wajen isar da ilmi, da suka hada da:

  • Tafarkin koyar da dalibai da malamai da kwadaitar da su wajen rubutu da haddace abubuwan da suka fito daga Ahlulbaiti (a.s) da kuma umartansu da yin ta'alifi da buga litattafa.

Shaikh al-Tusi cikin littafinsa na maruwaita ya ambato sunayen kimanin maruwaita dalibai da suka jiyo daga gare shi kimanin guda dari, cikinsu kuwa har da mata guda biyu.

Wadannan malamai dai sun ruwaito daga gare shi, kuma sun rubuta litattafa daban-daban a bangarorin ilmi daban-daban na Musulunci da assasa makarantun Islamiyya da ke karantar da asalin akidu na Musulunci.

  • Tafarkin ayyana wakilai da baza su yankuna daban-daban na duniyar musulmi don su kasance masu koyar da karantarwar Musulunci da hukumce-hukumcensa.

A irin wannan lokaci dai, Imam (a.s) ya kasance ya kan rubuta wa wadannan wakilai nasa da jin yadda lamurra suke gudana.

  • Tafarkin mukabala da tattaunawa ta ilmi kamar yadda litattafan hadisi da ruwayoyi suka gutsuro mana wasu daga cikin irin wadannan tattaunawa da hujjojin da ya kafa a wurare da dama don kare Musulunci da tabbatar da rukunansa a bangarorin tauhidi, fikihu, tafsiri, hadisi da dai sauransu.

Wadannan tattaunawa dai sun kasu kashi-kashi, wasu an yi su ne don kare Musulunci da mayar da martani a kan masu musanta Musulunci da sauran akidu na bata, wasu kuma don ingantar da tunanin wasu musulmi ne da suka yi riko da wasu karkatattun akidu irin 'yan gullatu da dai sauransu, wasu kuma don yin bayani kan wasu bangarorin Musulunci daban-daban.




____________