Haihuwar Imam Muhammad bn Ali Al-Jawad (a.s):

________________________

An haifi Imam Muhammand bn Ali al-Jawad (a.s), wato Imami na 9 daga cikin Imaman gidan Manzon Allah (s.a.w.a) ne a ranar 10 ga watan Rajab shekara ta 195 hijiriyya a garin Madina. Kuma ya tashi ne karkashin kulawar mahaifinsa Imam Ridha (a.s) wanda yake rike da nauyin imamanci, wato matsayin jagorancin al'umma.

Kimanin shekaru 40 na rayuwar Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s) suna kokarin wucewa amma dai har ya zuwa wannan lokacin Allah bai arzurta shi da da ba, wannan lamari dai ya sanya 'yan shi'a a wancan lokacin cikin damuwa da kuma addu'ar Allah Ya ba wa wannan shugaba na su da don ya gaje shi. Wannan damuwa ta 'yan shi'an kuwa ta biyo bayan kalaman da suka ji ne daga Imaman da suka gabata na cewa Imam na tara zai kasance da ne na Imami na takwas (Imam Ridha), to a halin yanzu dai ga Imam din ba shi da wani da. Wannan lamari dai ya sa har wasu daga cikin mabiya Imam Ridha din suna tambayarsa kan wanda zai gaje shi, inda a kowani lokaci ya kan amsa musu da cewa: "Allah Zai ba ni wani da da zai gaje ni kana kuma wanda zai zama Imami a bayana".

Hakan kuwa ya faru, don daga karshe dai an haifi Imam al-Jawad din a ranar goma ga watan Rajab shekara ta 195 bayan hijira, inda aka sanya masa suna Muhammad, alkunyarsa kuwa Abu Ja'afar ne. Mahaifiyarsa kuwa ita ce 'Subaika' (Khaizran) wacce take daga zuriyar Mariya al-Kibtiyya, matar Manzon Allah (s), wacce aka santa da tsoron Allah da halaye na kwarai.

Wannan haihuwa ta Imam al-Jawad (a.s) dai ta sanya farin ciki da murna tsakanin mabiya Ahlulbaiti (a.s) saboda daga karshe dai burinsu zai cika kana kuma wasu kuma da shakku ya fara shiga zukatansu su sami kwanciyar hankali yanzu.

Bari mu ji kadan daga cikin bayanai kan yadda wannan haihuwa ta kasance daga bakin daya daga cikin wadanda suka kasance a wurin.

An ruwaito Hakima, 'yar'uwan Imam Ridha (a.s) tana cewa a daren haihuwar Imam al-Jawad, dan'uwanta (Imam Ridha) ya umarce ta da ta kasance tare da matarsa (mahaifiyar al-Jawad) don kula da ita. Cikin wannan lokaci kuwa sai aka haifi Imam al-Jawad, bayan haihuwarsa dai sai Hakima ta ce ta ji shi yana Kalmar Shahada, wannan lamari dai ya ba ta mamaki sosai don haka sai ta ruga da gudu wajen Imam Ridha (a.s) don ba shi labarin abin da ta gani. Nan take sai Imam ya ce mata: "Ya 'yar'uwata, kada ki damu, za ki ci gaba da ganin abubuwan ban mamaki nan gaba"

Hakan kuwa ya faru don tun Imam al-Jawad yana karami ake ganin abubuwan mamaki da kuma kira zuwa ga binsa da mahaifinsa ya ke yi wa mabiyansa.

An ruwaito Naufali, daya daga cikin sahabban Imam Ridha (a.s) yana cewa: "Wata rana lokacin da Imam Ridha (a.s) ya fita don tafiya Khorasan, na ce masa: 'Babu wani umarni da za ka min, (Ya shugabana)?', sai ya ce masa: "Ka bi dana a bayana, kuma ka tambaye shi duk tambayar da ka ke da ita"

A lokuta da dama dai Imam Ridha (a.s) ya kasance yana gaya wa mabiyansa cewa: "Ba lalle sai kun dinga rubuto min da tambayoyi ba, a maimakon haka kuna iya tambayar wannan karamin yaro (yana nufin Imam al-Jawad) wanda zai kasance Imami a bayana"

A wasu lokuta ma dai wasu mutane sukan nuna mamakinsu da yadda karamin yaro zai zamanto shugaban al'umma. Imam dai ya kan amsa musu da cewa: Ai Allah ya nada Annabi Isa (a.s) a matsayin Annabi alhali shekarunsa ba su kai na Abu Ja'afar (Imam Jawad) ba. Lalle shekaru ba su da wani tasiri a bangaren annabci da imamanci.

An haifi Imam Jawad (a.s) ne a cikin zamanin da ke cike da lamurra da yanayi na siyasa, ga kuma rikice-rikicen cikin gida da neman mulki tsakanin Amin da Ma'amun ('ya'yan Haruna Rashid).

Babu shakka babu yadda za a iya cewa wannan yanayi na siyasa da rikice-rikice sun kare ba tare da sun taba rayuwar Imam Ridha da dansa Imam Jawad (a.s) ba. Irin wannan yanayi ne ma ya sa Ma'amun ya mayar da hankali a kan Imam Ridha (a.s) da dawo da shi helkwatar mulkinsa da ke Marwa, sai dai kuma duk da cewa Imam (a.s) daga farko ya ki amincewa, amma daga karshe ya amince bayan tursasawa mai tsananin gaske.

Kafin ya fita zuwa Marwan sai da Imam Ridha (a.s) tare da dansa al-Jawad (a.s) suka tafi Makka don ziyartar Dakin Allah mai tsarki da masa ban kwana, inda tare da dansa - wanda a lokacin yana dan kimanin shekaru hudu a duniya - suka yi dawafi na ban kwana.

Duk da irin wannan karancin shekaru da Imam Jawad (a.s) yake da shi, to amma ya ji dacin rabuwa da mahaifinsa ya kuma fahimci cewa ba za su sake haduwa da juna ba, ya fahimci cewa shi kadai ne fa zai dawo Madina, hakan kuwa ya biyo bayan irin ruhi da fahimtar da yake da shi da ba kowa ne aka ba shi irinta ba in ba shi ba sai dai sauran Imamai daga zuriyar Manzo mai tsira da aminci.

Bayan gama dawafin ban kwana, yanzu kuma lokaci ne na rabuwa, inda Imam al-Jawad ya kama hanyar Madina cikin tunani da kaunar mahaifinsa shi kuma ya kama hanyar zuwa garin Marwa.

Kwance tashi dai Imam Ridha (a.s) ya isa garin Marwa helkwatar mulkin Abbasiyawa a wancan lokacin, alhali zuciyarsa na cike da tunanin dansa al-Jawad (a.s). Don haka ya ci gaba da aike masa da wasiku don ci gaba da nuna kulawa da shi da kuma tarbiyyantar da shi. Malaman tarihi sun ruwaito cewa Imam Ridha (a.s) ya kan yawaita rubuta masa wasika cikin girmamawa yana mai kiransa da sunan Abu Ja'afar.






____________