Yanayin Siyasa A Lokacin Imam Hadi (a.s):

________________________

Rayuwar Imam al-Hadi (a.s) dai cike take da cutarwa irin ta siyasa, don kuwa ya rayu ne tare da sarakunan Abbasiyawa masu tsananin gaba da 'ya'yan Fatima al-Zahra, 'yar Manzon Allah (s.a.w.a).

Imam al-Hadi (a.s) ya rayu cikin sauran lokacin mulkin Mu'utasim al-Abbasi, sai kuma shekara biyar da watanni tara na mulkin al-Wasik, sai kuma shekaru goma sha hudu da watanni goma na mulkin Mutawakkil, da watanni shida na mulkin Muntasir, sai kuma shekaru hudu na mulkin Musta'in, sai kuma shekaru hudu da wata hudu na mulkin Mu'utaz, wanda Imam (a.s) ya yi shahada a karshen mulkinsa.

Wadannan shekaru dai cike suke da abubuwa da rikice-rikicen siyasa daban-daban tsakanin Alawiyyawa (mabiya Ahlulbaiti) da Abbasiyawa, inda Abbasiyawan suka cutar da Imam (a.s) nesa ba kusa ba. A wannan lokacin dai Abbasiyawan sun kasance cikin tsoron Imam al-Hadi (a.s) saboda kasantuwansa shugaban Ahlulbaiti kana kuma jagoran al'umma, kuma mai fadi masu su ji.

Kamar dai kowani lokaci, Ahlulbaiti (a.s) sun kasance suna da matsayi mai girman gaske a zukatan al'umma, kamar yadda suke da kyakkyawar alaka tsakaninsu da su sama da yadda suke da shi da mahukuntan Abbasiyawa saboda zalunci da zubar da jininsu da suka dinga yi sannan kuma ga irin zurfin da suka yi wajen sabon Allah da almubazzaranci da dukiyar al'umma duk kuwa da cewa al'ummar suna cikin halin talauci da matsi na tattalin arziki sakamakon takurawar mahukuntan.

Imam al-Hadi (a.s) ya kasance ya dauki nauyin wayar da kan al'umma a bangare siyasa da imani ta hanyar janyo mutane zuwa gare shi da tarbiyyantar da su da fahimtar da su tsarkakakken Musulunci, addini na hakika da kuma ra'ayin Musulunci kan jagoranci da kuma siyasa.

Irin wannan yanayi da nauyin wayar da kan al'umma da Imam al-Hadi (a.s) ya ke ya sanya mahukuntan Abbasiyawa cikin damuwa da tsoron Imam, don haka suka sanya shi karkashin kulawa da sanya ido don tattara bayanai da za su ba su daman dakatar da wannan aiki nasa da kuma raba shi da al'umma da kuma ayyukan siyasa.

Dubi cikin rayuwar Imam al-Hadi (a.s) tun bayan shahadar mahaifinsa da kuma daukan nauyin jagorantar al'umma har lokacin shahadarsa, za mu ga cewa rayuwarsa tana cike ne da barazana, hakuri da kuma tsayin daka na akida da siyasa. Imam al-Hadi (a.s) ya gamu ne da mahukunta masu tsananin adawa da zuriyar Abu Talib (a.s) musamman zuriyar Ali da Fatima al-Zahra da (a.s) da kuma kokarin ganin bayansu.

Imam al-Hadi (a.s) ya fara ayyukansa na siyasa ne dai a karshe-karshen zamanin sarki Mu'utasim al-Abbasi, wanda ya kasance mai cutar da Ahlulbaiti da dukkan wani mai adawa da mulkinsa na zalunci. Fasadi dai ya zama ruwan dare gama duniya, azzalumai marasa imani kuwa su ne suke rike da al'amurran mulki da gudanarwa, sannan shi ma Mu'utasim din kamar iyayensa da suka gabata babu abin da ya sa a gaba in ban da wasa, wargi, almubazzaranci da kudin al'umma, zubar da jininsu, ta yadda hatta malaman tarihi sun bayyana shi da cewa: "Idan ya yi fushi, to fa bai damu wa ya kashe ko kuma mai ya aikata ba(1)".

Suyuti ya hakaito kadan daga cikin alamun fasadinsa da cewa:

"Yana da wani yaro da ake ce ma Ajib, ya kasance yana tsananin son yaron ta yadda har yake tsara masa waka(2)".

Saboda irin tasirin da Imam al-Hadi (a.s) ya ke da shi ne ya sanya wata rana Mu'utasim ya kira shi daga Madina zuwa Bagadada, ya kuma tilasta masa zama a wajen har lokacin da ya aka sanya masa guba da kuma wafatinsa kamar yadda wasu malaman tarihi suka ruwaito.

Daga nan sai Mu'utasim ya gina garin Samarra da kuma mai da wannan gari a matsayin helkwatar mulkinsa kana kuma barikin sojojinsa, don haka ne ma ake kiran garin da al-Askar, kuma ake kiran Imam al-Hasan al-Askari da wannan suna saboda zaman da ya yi a wajen daga baya.

Wani abin da ke nuni da irin zaluncin Mu'utasim shi ne umarnin da ya yi na a kamo Ahmad bn Hambal, limamin mazhabar Hanbaliyya, ya yi masa dukkan tsiya ta yadda har ya fita daga hankalinsa kana ya sa aka rufe a daddaure. Hakan kuwa ya biyo bayan bayyana ra'ayinsa ne da ya yi kan halittan Alkur'ani wanda ya saba wa ra'ayin Mu'utasim din(3)".

Bayan mutuwar Mu'utasim sai dansa al-Wasik ya gaje shi a shekara ta 227 hijiriyya, to shi ma dai al-Wasik ba shi da wani banbanci da mahaifinsa a bangare siyasa da kuma mu'amala da talakawansa, sai dai kawai malaman tarihi sun bayyana cewa a lokacinsa ya dan raga wa Ahlulbaiti, bai kashe guda daga cikinsu ba, hakan kuwa ya biyo bayan shagaltuwa da ya yi ne da wasanni da fasadi.

A daidai wannan lokaci dai Imam al-Hadi (a.s) ya zauna a Madina yana ta karantar da al'umma, bautar Allah, shiryar da mutane alhali kuwa yana cikin shekarunsa na samartaka. A wannan lokacin dai tauraruwarsa ta haska sosai, sannan kuma matsayinsa ya daukaka, bugu da kari kan matsayin da ya samu a zukatan al'umma.




____________
1- Tarikh al-Rusul wa al-Muluk na Tabari, juzu'i na 7, shafi na 316.

2- Tarikh al-Khulafa' na Suyuti, shafi na 381.

3- Tarikh al-Ya'akubi na Al-Ya'akubi, juzu'i na 2, shafi na 472 da al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 6, shafi na 445.