Shahadar Imam Ali bn Muhammad al-Hadi (a.s)

 

 

 

Rayuwar Imam al-Hadi (a.s) dai ta kasance rayuwa ce da take cike da ilmi, aiki da kira zuwa ga Littafin Allah da Sunnar ManzonSa (a.s), kamar yadda kuma ta kasance rayuwa ce mai cike da rikice-rikicen siyasa a kokarin da yake yi na tabbatar da gaskiya da taimakon wadanda aka zalunta.

Irin wannan rayuwa tasa dai ta fuskanci takuri da kuma ta'addanci mahukuntan wancan lokaci, inda suka fitar da shi daga Madina da tilasta masa zama a garin Samarra don ya kasance karkashin kulawa da sanya ido da hana shi gudanar da wadannan ayyuka nasa. Ya shafe lokaci mai yawa na rayuwarsa a garin Samarra har lokacin da ya yi shahada sakamakon guban da aka sanya masa a watan Rajab shekara ta 254 hijiriyya lokacin mulkin Mu'utaz, a lokacin kuwa yana da shekaru 41 a duniya. Kabarinsa yana garin Samarra, inda a kullum al'umma ke ziyartarsa da kuma girmama shi.

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, ranar da ya yi shahada da kuma ranar da za a tashe shi rayayye wanda aka zalunta.