Hijirar Imam al-Hadi (Daga Madina Zuwa Samarra):

________________________

Duk da irin wannan hali dai, Imam al-Hadi (a.s) bai gafala da irin wannan mulkin zaluncin da suke fuskanta ba daga Mutawakkil al-Abbasi, don haka ya ci gaba da kokarin karfafa alakarsa da al'umma da yada koyarwa ta Musulunci da tarbiyyantar da malamai da gina su a kan tafarkin ilmi, takawa, tsantsaini da kuma tabbatuwa akan gaskiya da fada da zalunci.

To sai dai lokacin da irin wannan tasiri da Imam ya ke samu tsakanin al'umma a garin Madina ya dada karuwa kana kuma hakan ya kasance babban hatsari ga Mutawakkil da mulkinsa, sai ya fara makirce-makircen ganin bayan Imam (a.s).

Masu adawa da Imam din dai daga cikin na kurkusa da Mutawakkil sun ta kokarin kai suka da tabbatar masa da cewa Imam (a.s) babban hatsari ne ga mulkinsa, yana can yana ta tara kudade, makamai da jama'a don fuskantarsa. Don haka sai Mutawakkil ya kira Imam (a.s) daga Madina zuwa garin al-Askar (Samarra) don sanya shi karkashin kulawan 'yan leken asiri dare da rana, hakan kuwa ya faru ne a shekara ta 243 hijiriyya.

Rubuce-rubuce da littattafan tarihi sun yi nuni da dalilan da suka sa Mutawakkil ya kira Imam zuwa Samarra, daga ciki kuwa shi ne abin da Yazdan, likitan fadan Abbasiyawa, ya fadi wa Isma'il Kahkali: "Labari ya zo min cewa Halifa ya kirayi -al-Hadi - daga Hijaz saboda tsoronsa da ya ke yi, don kada mutane su koma gare shi kana kuma mulki ya kubuce daga hannunsa (Mutawakkil)(1).

"Sibt Ibn al-Jawzi yana cewa: Labarin matsayin Aliyu (al-Hadi) a zukatan al'ummar Madina ya iso masa (Mutawakkil) don haka tsoronsa ta kama shi(2)".

Bayan isowar Imam (a.s) garin Samarra, mahukunta sun fara gudanar da siyasarsu ta takurawa da kuma sanya ido kansa da mabiyansa; a wasu lokuta sukan yi kokari wajen zubar da mutumcinsa, wasu lokuta kuma ta hanyar kame shi da kuma tsarewa, a wani lokacin kuma ta hanyar kai samame gidansa da kuma binciken gidan, wata rana su kama shi suna zarginsa da shirya yunkurin kawar da halifa, a wasu lokutan kuma su yi kokarin samar da wani mutum da zai maye gurbin Imam din (a.s). To sai dai kuma dukkan wadannan kokari da makirce-makirce su kan kare ba tare da cin nasara ba, don kuwa kulawar Ubangiji tana tare da Imam kana kuma tana kare shi daga sharrinsu, a waje guda kuma matsayi da daukakar Imam sai dada karuwa take yi a zukatan mutane.

Shaikh Tabrisi yana cewa: "Mutawakkil ya yi ta kokarin kulla makirce-makirce da kuma kokarin sanya daukakarsa a zukatan al'umma, to sai dai kuma hakan bai faru ba(3)".

Haka dai wannan yanayi na rikici tsakanin Mutawakkil da Imam al-Hadi (a.s) ya ci gaba har lokacin da aka kashe Mutawakkil a shekara ta 247 hijiriyya, lokacin da dansa Muntasir ya shirya kashe shi alhali yana cikin maye a fadar mulkinsa. Daga nan sai dan nasa al-Muntasir ya dare karagar mulki, a lokacinsa dai Ahlulbaiti da mabiyansu sun dan samu sauki saboda saukaka musu rayuwa da ya yi da kuma mayar musu da wasu hakkokinsu da aka kwace.

Mulkin Muntasir dai bai jima ba, don kuwa ya mutu a shekara ta 248 hijiriyya, daga nan sai Musta'in ya dare karagar mulki, a lokacinsa dai fitinu sun yi yawan gaske, inda al'umma suka kai hari kan gidajen yarin garuruwan Bagadada da Samarra da kuma sake fursunonin da suke ciki.

Irin wadannan rikice-rikice dai sun sanya aka kashe Muntasir kamar Mutawakkil a shekara ta 252 hijiriyya, inda aka dauki kansa aka kai wa al-Mu'utaz (wanda ya gaje shi) a lokacin yana dara, sai ya ce: "Ku ajiye shi har sai na gama abin da nake, bayan ya gama sai ya yi umarnin da a bisne shi(4). Shi ma dai Mu'utaz bai kasance ya gaza halifofin da suka gabace shi ba wajen zalunci, don kuwa yanayi ya kara lalacewa ne a lokacinsa.




____________
1- Bihar al-Anwar na Majlisi, juzu'i na 50, shafi na 161.

2- Tazkirat al-Khawas na Sibt Ibn al-Jawzi, shafi na 359.

3- A'alam al-Wara bi A'alam al-Huda na Tabrisi, shafi na 360.

4- Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 7, shafi na 173.