|
|
| |||
|
________________________
Al-Mutawwakkil, Ja'afar bn al-Mu'utasim, ya dare karagar mulki bayan mutuwar al-Wasik a shekara ta 232 hijiriyya, to sai dai kuma fa Ahlulbaiti da mabiyansu sun fuskanci tsanani da matsin lamba daga gare shi tun bayan darewarsa karagar mulkin.
Ga kadan daga cikin irin adawar da Mutawakkil ya nuna wa Ahlulbaiti (a.s) a lokacin mulkinsa:
Har ila yau daga cikin halin zalunci da aka fuskanta a wannan lokaci har da abin da Abul Faraj al-Isfahani ya fadi:
"Mutawakkil dai ya kasance mai tsanani ga Ahlulbaiti, mai adawa da su da mabiyansu, mai sanya idanuwa kan abubuwan da suke gudanarwa, mai tsananin zargi da tuhumarsu….abubuwan da ake kawo masa dangane da su ya fi na dukkan sarakunan
Abbasiyawa da suka gabace shi. Daga cikin irin abubuwan da ya aikata kuwa har da ruguza kabarin al-Hasan da shafe alamarsa, haka kuma ya sanya sansanonin bincikensa a dukkan hanyoyin zuwa kabarin, babu wani mutum da zai kawo ziyara face sai an kawo
masa shi, ya kashe shi ko kuma ya azabtar da shi(1)".
Da dama daga cikin malumman tarihi sun ruwaito irin siyasar zalunci ta Mutawakkil da kuma irin takurawa Ahlulbaiti da mabiyansu da ya yi.
Haka nan kuma al-Isfahanin ya nakalto kadan daga cikin halin kuncin da Ahlulbaiti da mabiyansu suka shiga tare da mata da 'ya'yayensu sakamakon siyasar zaluncin Mutawakkil, inda ya ke cewa:
"An dora Umar bn al-Faraj al-Rakhji a matsayin hakimin Makka da Madina, don haka sai ya hana Ahlulbaiti gudanar da ayyukan al'umma kamar yadda kuma ya hana al'umman komawa gare su da kuma taimaka musu, ta yadda babu wani mutumin da zai
taimaka musu face sai ya yi masa azaba mai tsanani. Lamari dai ya kai ta yadda hatta tufafin salla mataye sun rasa su saboda takuri har lokacin da Mutawakkil ya mutu(2)".
|
||||