|
|
| |||
|
________________________
An haifi Imam Aliyu al-Hadi (a.s) ne a wani yanki na garin Madina da ake kira da 'Saryah' a tsakiyar watan Zil Hajji shekara ta 213 hijiriyya.
Ya rayu da kuma girma ne karkashin kulawar mahaifinsa Imam al-Jawad (a.s), inda ya gaji ilmi da dabi'un Ahlulbaiti (a.s) daga wajensa. Tun dai kafin shahadar
mahaifinsa, ya tabbatar da cewa: "Jagoranci bayana zai koma ne ga dana Aliyu(1)".
Imam al-Hadi (a.s) dai yana daga cikin Imaman Ahlulbaiti (a.s) da suka gaji imani, ilmi, halaye na gari da kuma takawa daga baba zuwa kaka zuwa Manzon Allah
(s.a.w.a), don haka ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi mana wasiyya a kansu da cewa:
"Lalle ni na bar muku nauyaya guda biyu: Littafin Allah da zuriyata Ahlulbaiti, idan kuka yi riko da su to lalle ba za ku taba bata ba(2)".
Haka nan kuma Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa:
"Mu Ahlulbaiti ba a kwatanta mu da wani".
Imam al-Hadi (a.s) dai ya kasance abin koyi cikin kyawawan halaye, gudun abin duniya, ibada, fada da zalunci da kuma fuskantar azzalumai, fitilar ilmi, aiki da kuma kula, don haka
ne malamai, masana da 'yan siyasa suke girmama shi da siffanta shi da siffofi na yabo. Abu Abdullah al-Junaid yana cewa: "Wallahi shi ne mafi alherin mutanen duniya kana kuma wanda ya fi
kowa -daga cikin mutanen zamaninsa-(3)".
Irin matsayin da Imam al-Hadi (a.s) yake da shi abu ne dai da yake a fili da ba za a iya boye shi ba hatta masu adawa da Imam din daga cikin mahukuntan wancan lokacin, wadanda suka
gane wa idanuwansu abin da suka gani na imani da takawar Imam (a.s) a lokacin da suka kai masa hari a gidansa da daddare suna nuna cewa:
"Sun kai hari gidansa amma dai ba su sami komai ba, sun same shi a gidan ne a rufe, yana zaune akan turbaya da tsakuwa, alhali yana karanta Alkur'ani mai girma(4)".
"Ta haka ne suka kama shi zuwa wajen halifan Abbasiyawa al-Mutawakkil, inda suka shiga da shi alhali Mutawakkil din yana zaune a wajen shan giyansa. Sai ya miko wa Imam kofin giya, amma sai Imam ya ce
masa: "Wallahi tsoka da jinina bai taba gamuwa da giya ba, ka min afuwa", sai ya yarda amma sai ya ce masa ka rera min waka, sai Imam (a.s) ya ce masa: "Ai ni ba mawaki ba ne", sai ya ce lalle babu makawa sai ka rera
min waka. Don haka sai Imam (a.s) ya rera masa wadannan baitoci na waka:
Sun shafe dare a saman dutse don su kare kansu,
Sai dai an galabci duwatsun, ba su kare su ba.
Bayan daukaka, an kawar da su daga mulkinsu,
Aka sanya su cikin rami, makomarsu, ta munana.
Wani mai kira ya kira su, bayan an bisne su,
Ina ababen wuya, kanbin sarauta da manyan kaya.
Ina fuskokin nan da suka kasance cikin ni'ima,
Wadanda aka rufe su da labule da abin kare sauro.
Kabari ya yi magana a kansu lokacin da aka tambayesu,
Tsutsotsi na nan na kokawa da wadannan fuskoki.
Sun kasace suna ci da sha na tsawon lokaci,
Bayan dogon ci ga shi yanzu su ma ana cinsu.
Nan take sai Mutawakkil da wadanda suke wajen suka fashe da kuka(5).
Dubi cikin wannan wadannan abubuwa da suka faru zai dada tabbatar mana da matsayin da Imam (a.s) ya ke da shi, bugu da kari kan ibada, tsantsaini, damfaruwar al'umma da kuma girmama shi da suke yi, don ya kasance
ma'abucin ibada, nesantar duniya. Wannan lamari ne dai da kowa da kowa ya san shi da shi hatta masu adawa da shi.
|
||||