Hakika irin yanayi na siyasa da kuma dabi'ar masu mulki, sun taimaka nesa ba kusa ba wajen haifar da kungiyoyi da yunkure-yunkuren 'yan adawa, wadanda suke kira da a dau makami don fuskantar mahukunta. Don haka mabiya Ahlulbaiti sun shirya
yunkure-yunkuren fuskantar mahukunta a zamanin Imam al-Hadi (a.s).
Kusan dukkan wadannan yunkure-yunkure kuwa suna kira ne zuwa ga komawa ga Imaman Ahlulbaiti karkashin jagorancin Imam na lokacin wato al-Hadi (a.s), kuwa dukkan wadannan yunkure-yunkure sun kasance ne lokacin mulkin Musta'in
har zuwa lokacin da aka kashe shi kana Mu'utaz ya dare karagar mulki.
Mulkin Mu'utaz dai cike yake da zalunci da lalacewar yanayin siyasa a garuruwan Bagadada, Samarra da sauran garuruwan da suke karkashin mulkinsa, sama da lokacin wadanda suka gabace shi.
Duk tsawon wannan lokaci dai, Imam al-Hadi (a.s) ya kasance yana darasin yadda lamurra suke gudana, don haka ya yi ta kokarin rage zaluncin Abbasiyawa da kuma ba da himma wajen yada ilmi da kare asasin shari'ar Musulunci da
kuma tarbiyyar al'umma, wayar da kan al'umma da fahimtar da su addini na hakika ba irin wanda Abbasiyawa suka lalata da tilasta wa al'umma don tabbatar da mulkinsu ba.
Ta haka ne Imam al-Hadi (a.s) ya ci gaba da wannan aiki na yada ilmi da wayar da kan al'umma da imaman da suka gabace shi suka faro, bugu da kari kan tsarkake addini bayan da mahukunta da muggan malamai sun bata shi.
Babban kokarin Ahlulbaiti (a.s) dai shi ne kiyaye shari'ar Musulunci da gabatar da ita a tsarkake kamar yadda Manzo (s.a.w.a) ya zo da ita. Don haka ne suka ba da muhimmaci su da dalibansu wajen cimma wannan manufa. Shaikh
al-Tusi ya ruwaito cikin littafinsa na maruwaita hadisai kimanin dalibai da maruwaita dari da tamanin da biyar da suka ruwaito hadisai daga Imam al-Hadi (a.s).
____________