|
|
| |||
|
________________________
Imam Bakir (a.s) dai ya zama cikin shiri da kuma shiryawa don kamala aikin da mahaifinsa Imam Sajjad (a.s) ya fara na aikin kawo canji ta hanyar siyasa da koyarwa, ta haka ne ya gudanar da ayyukansa na wayar da kan al'umma wajen
yin hidima wa Musulunci don cimma manufar aiko Manzon Allah (s.a.w.a).
Ayyukan Imam (a.s) sai dada karuwa suke yi a bangaren ilmin Musulunci, lamarin da ya sanya al'ummomi daga dukkan bangarori na duniyar musulmi da suka hada da dalibai da masu neman tattaunawa daga Mu'utazilawa,
Hawarijawa da dai sauransu suka tuttudo wajensa don amfanuwa da dimbin ilminsa da kuma neman karin bayani kan abubuwan da suka shige musu duhu.
Mazhabar Ahlulbaiti (a.s) a lokacin Imam Bakir (a.s) ta kebantu da wasu abubuwa kamar haka:
Shaikh al-Mufid na cewa:
"Ilmin addini, sunna, Alkur'ani da tarihi da kuma sauran fannoni bai bayyana wajen daya daga cikin 'ya'yayen Hasan da Husaini (a.s) ba kamar yadda ya bayyana daga wajen Abu Ja'afar al-Bakir (a.s)".
Abu Ja'afar (a.s) ya ruwaito labaran Annabawa, sannan kuma mutane sun samo sunna daga gare shi, sun kuma dogara gare shi wajen ayyukan hajjin da ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a), sun kuma rubuta tafsirin Alkur'ani
daga gare shi, kamar yadda shi'a da sunna duk sun ruwaito daga gare shi, sannan kuma ya yi tattaunawa ta ilmi da wadanda suke da sabanin ra'ayi da shi na daga malamai, kamar yadda kuma mutane sun samo da haddace ilmin
tauhidi mai yawa daga wajensa(1)
Dangane da irin ilmi da hangen nesan Imam (a.s), daya daga cikin almajiransa Muhammadu bn Muslim yana cewa: "Ba wani abin da ya taba zuwa min (da ban fahimce shi ba) da ban tambayi Abu Ja'afar (a.s) ba, na tambaye shi
kimanin mas'aloli dubu talatin((2)
Kamar yada Imam (a.s) ya mallaki nau'oi daban-daban na ilmi da masaniyya, haka kuma yake da hanyoyi daban-daban na bayyanar da ilmi da kuma ra'ayin Musulunci kan mas'aloli daban-daban. A wani lokaci ya kan gabatar da shi
ne ta hanyar koyarwa kamar yayin da yake koyar da dalibansa, a wani lokacin kuma ta hanyar tattaunawa ta ilmi da masu sabanin ra'ayi da shi, a wani lokacin kuma ta hanyar ganawa ta gaba daya kamar lokacin aikin hajji da makamancin haka,
a wani lokacin kuma ta hanyar kalamai, wasiyyoyi da kuma wa'azi da dai sauransu.
Dubi da idon basira cikin abin da litattafan tarihi suka tanadar mana kan Imam Bakir (a.s) za mu iya ganin jerin sunayen littattafa da rubuce-rubuce da suke kunshe da wayewa irin ta Musulunci da suke komawa ga makarantar Imam Bakir (a.s).
Gwarzayen Musulunci daga sauran sahabbai, tabi'ai da manyan shuwagabannin fikihun Musulunci sun ruwaito daga gare shi, ta haka ne ya zamanto gwarzo da ake misali da shi(3)
Gidan Imam (a.s) da ke Madina dai ya zamanto wata cibiya ta shiryarwa da daukaka da dalibai suke tuttudowa daga sauran kasashe, kamar yadda kuma Imam (a.s) ya ke amfani da lokutan bukukuwa wajen isar da sakon da ya ke son ya isar musu.
|
||||