|
|
| |||
|
________________________ A baya mun bayyana cewar mahukuntar Abbasiyawa sun rayu ne cikin zaluntar al’umma da kuma aikata nau’oi daban-daban na fasadi da lalacewa, sannan kuma mun ga cewa Imam al-Askari (a.s) ya rayu ne lokacin mulkin Mutawakkil da dansa Muntasir da kuma Musta’in, kana daga baya kuma ya zama Imami kuma jagoran al’umma bayan wafatin mahaifinsa a shekara ta 254 hijiriyya a lokacin mulkin Mu’utaz al-Abbasi wadanda Turkawan da suke kusa da shi suka yi waje da shi a shekara ta 255 hijiriyya da kuma tsare shi har ya mutu bayan ‘yan kwanaki. Daga nan kuma sai Al-Mahdi al-Abbasi ya dare karagar mulki wanda shi ma ya fuskanci irin wannan matsalar, inda suka kai masa hari da raunana shi da kuma kiransa da ya sauka daga mulki amma dai ya ki amincewa da hakan, inda shi ma ya mutu bayan kwanaki biyu a shekara ta 256 hijiriyya. Wannan dai shi ne yadda yanayi ya kasance a bangaren mahukunta kenan. Bangaren talakawa kuwa, malaman tarihi sun bayyana cewa wata annoba ta bullo a Iraki a shekata ta 258 hijiriyya inda ta kashe dubban mutane, sannan kuma ga talaucin da ya yi wa mutane kanta bugu da kari kan tsadan kayayyaki, ‘ta yadda saboda tsadan kayayyaki a Makka mutane suka fice suka nufi garuruwan da ke makwabtaka da garin…a Bagadada ma farashin kayayyaki ya tashi sama([1])”. Al-Ya’akubi ma ya ruwaito wani sashi na irin wannan yanayi da ake ciki inda ya ce: “Kudaden kayayyaki sun yi tashin gwauron zabbi a garuruwan Bagadada da Samarra….ga kuma karancin kudade a hannun al’umma([2])”. A daidai lokacin da al’umma suke fuskantar talauci, yunwa da cututtuka da kuma zalunci irin na mahukunta, a bangare guda kuma mahukunta suna cikin jin dadi da wasa da dukiyar al’umma, fadojinsu da kewayensu cike suke da kayayyakin wasa da wargi da fasadi, matayensu suna cikin kudi, an ce dukiyoyin da matayensu kawai suka mallaka sun kai miliyoyi kamar yadda abin da suke kashewa a shekara ma sun kai wasu miliyoyin. Dangane da hakan an ruwaito cewa:
“Ummu
Muhammadu bn al-Wasik – halifan lokacin – ta mutu tun kafin a yi masa mubaya’a,
ta kasance ne karkashin kulawar Musta’in, bayan da aka kashe Musta’in, Mu’utaz
ya ajiye ta cikin fadar sarki, wata rana bayan darewarsa mulki ya ce wa wasu
daga cikin mabiyansa cewa: “Ni kan bani da wata mahaifiya da zan bukaci in
kashe mata dirhami miliyan goma a kowace shekara don ta kashe wa bayi da masu
mata hidima”.
Malaman tarihi sun nakalto
cewa Kabihah, daya daga cikin bayin Mutawakkil kuma uwar dansa Mu’utaz, ta
tattara dukiyarta daga Bagadada zuwa
([2])
Tarikh al-Ya’akubi na Ya’akubi, juzu’i na 2, shafi na 499.
([3]).
Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu’i na 7, shafi na 200. |
||||