|
|
| |||
|
________________________
Imam Hasan
al-Askari (a.s) ya yi zamani ne da sarakunan Abbasiyawa irin su Mu’utaz,
Muhtadi da Mu’utamid, inda ya fuskanci matsin lamba da takurawa mai girman
gaske daga wajen wadannan sarakuna (halifofi) guda uku, kamar yadda kuma suka
sha
Sarki na karshe da Imam al-Askari (a.s) ya rayu
da shi shi ne Mu’utamid wanda ya kasance mai son wasa, wargi, kide-kide da
shaye-shaye, lamarin da ya sanya al’umma suka ki shi ki na gaske([1]).
A wannan lokaci kuwa Imam (a.s) ya fuskanci matsin
lamba mai tsananin gaske daga Mu’utamid da kuma sanya idanuwa
Ba komai ya sa shi da sauran Abbasiyawa daukan
wannan kakkausar mataki ba face dai irin gaba da hassadan da suke yi kan
matsayin da Imam (a.s) yake da shi a zukatan al’umma da kuma tsoron da suke
ciki na haihuwar dansa Imam al-Mahdi (a.s), wanda tuni daman sun riga da sun
san cewa zai kasance ne daga tsatson([3])
Imam al-Askari (a.s). Imam al-Askari (a.s) ya yi nuni da wannan batu cikin wata
wasikarsa inda ya ce:
“Suna tunanin kashe ni don su kawo karshen
wannan zuriya, lalle Allah Ya karyata wannan zance nasu, godiya ta tabbata ga
Allah([4])”.
Hassada da gaban Mu’utamid dangane da irin kaunar da al’umma
suke nunawa Imam (a.s) sai dada karuwa suke yi, alhali a kullum al’umma sai kara
tsanansa suke yi, don haka sai ya yanke shawarar
Hakan
kuwa ya faru, don ya sanya masa guba mai tsananin gaske cikin abincinsa inda ya
yi kwanaki yana kwance cikin halin rashin lafiya mai tsanani sai dai kuma ya yi
hakuri da kuma neman kusanci da Allah Madaukakin Sarki([5]).
Inda ya yi shahada a shekara ta 260 hijiriyya alhali yana dan shekaru ashirin
da takwas. Amincin Allah ya tabbata a gare shi, ranar da aka haife shi, ranar da ya yi shahada da ranar da za a tashe shi a matsayin wanda aka zalunta.
([1]).
Hayat al-Imam al-Askari na Bakir Sharif al-Karshi, shafi na 255, yana
mai nakaltowa daga Tarikh al-Khulafa’, shafi na 363.
([3]).
Bisa hadisan da suka zo daga Manzon Allah (s.a.w.a) |
||||