Imam Al-Askari Wajen Fuskantar Dawagitai (a.s):

________________________

Mahukuntan Abbasiyawa sun dau matakan takurawa Imam al-Askari (a.s) ta hanyar sanya ido kansa da ayyukan da yake gudanarwa, da nufin kawo karshen ayyukansa da kuma hana shi ba da gudammawarsa ta jagoranci da shiryar da al’umma…..

Don haka Imam al-Askari (a.s) ya zabi tafarkin gudanar da ayyukansa a asirce ba tare da ‘yan leken asirin Abbasiyawa sun gane ba, ta hanyar zaban wasu wakilai da za su gudanar da ayyuka da yawunsa da dai sauran hanyoyin da ya bi da tarihi ya tabbatar mana da su. Bari mu kawo kadan daga cikinsu:

1- Abu Hashim al-Ja’afari ya ruwaito daga Dawud bn al-Aswad da Kaddam, daya daga cikin masu hidima wa Imam (a.s) cewa:

“Wata rana shugabana Abu Muhammadu (Imam al-Askari) ya kira ni ya bani wani katako (ice) kamar kafar kofa mai tsawo, ya ce min: Ka kai wannan katakon ga al-Amri.

Sai na karba na ci gaba da tafiya, a kan hanyata sai na ci karo da wani mai bayin ruwa tare da alfadarinsa, sai wannan alfadari ya tsare min hanyar wucewa, sai mai alfadarin ya ce min in masa tsawa don koro masa shi, maimakon haka sai na dauki wannan katako na bugi alfadarin nan da shi, sai katakon ya tsage. Ko da na dubi katakon sai na ga takardu a ciki, nan take sai na tattara wannan katako da rike shi. Ganin haka sai wannan mutum ya kira ni yana ta zagina.

Koda na dawo sai Isa mai hidima ya tarbe ni bakin kofa, ya ce: shugabanmu yana ce maka: Me ya sa ka bugi alfadarin nan (da katakon) har ka karya shi.

Sai na ce masa: Ya shugabana! Ban san abin da ke cikinsa ba ne.

Sai ya ce: To amma me ya sa ka nemi yin musu kan abin da za ka nemi uzuri bayan ka aikata shi, ina gargadinka da ka da ka sake aikata hakan, idan ka ji wani yana zaginmu ka ci gaba da abin da aka umarce ka da aikatawa, kuma ina gargadinka da kada ka tanka wa wani wanda ya zage mu, ko kuma ma ka bayyana masa kai wane ne. Muna kasa ce da zalunci ya yi wa kanta, ka ci gaba da tafiyarka, don kuwa labarinka da halin da kake ciki duk yakan iso gare mu, lalle ya kamata ka san haka([1])”.

2- Daga Muhammadu bn Abdul’aziz al-Balkhi, yace:

“Wata rana da safe na zauna a bakin hanya, sai ga Abu Muhammadu (Imam al-Askari) (a.s) ya fito daga gidansa……, sai na ce a cikin zuciyata: Idan na ce Ya ku jama’a, wannan hujjar Allah ne a kanku don haka ku san shi, za a kashe ni?

Lokacin da ya matso kusa da ni, sai ya yi ishara da yatsarsa manuniya: da in yi shiru.

A wannan daren sai na ganshi yana ce min: “Abin dai ko boyewa ne ko kuma kisa, don haka ka ji tsoron Allah a kan kanka.



([1]). Manakib al-Abi Talib  na Ibn Shahr Ashub, juzu’i na 4, shafi na 427.