|
|
| |||
|
________________________ Babban aikin Imam (a.s) shi ne kiyaye sakon Musulunci, kira zuwa gare shi da kuma yada koyarwarsa. Don haka a tafarkinsa (a.s) cike ya ke da kiran mutane zuwa ga Musulunci da kuma kare shi daga masu adawa da shi da masu kokarin dasa sabbin abubuwa a cikinsa. Mafi girman tafarkin da ya dauka don cimma wannan manufa kuwa shi ne tafarkin koyarwa da ba da ilmi. Imam al-Askari (a.s) ya kasance yana da almajirai da maruwaita da yawa, wasu tun zamanin mahaifinsa suke gudanar da wannan aiki, wasu kuma sun hadu da shi ne a lokacin imamancinsa. Wadannan dalibai da maruwaita dai sun kasance masu ruwaito hadisai da karban ilmummuka daga gare shi. Shaikh al-Tusi ya ruwaito sunayen maruwaita casa’in da tara da suka ruwaito hadisai daga Imam Askari (a.s). Irin wadannan malamai da maruwaita da suka ruwaito daga Imam al-Askari (a.s) da kuma yin karatu a wajensa da iyayensa (a.s), sun ba da gagarumar gudummawa wajen watsa ilmin fikihu, tafsiri, hadisi, akida, adabi, ilmin yanayi da dai sauran ilmummuka.
Wadannan
abubuwa dai suna nuni ne da irin girma da fadin wannan makaranta ta Imam
al-Askari (a.s), kamar yadda kuma suke nuni da irin matsayin da Imam din ya ke
da shi a bangaren ilmi da masaniya. |
||||