Ibadar Imam Hasan bn Ali Al-Askari (a.s):

________________________

Tarihi da hadisai cike suke da bayanai kan ibadar Imam Askari, zuhudu da takawarsa, ga kadan daga ciki:

1-  Muhammadu al-Shakiri yana cewa: “Imam (a.s) ya kasance ya kan yi sujada a wajen sallarsa har in yi barci in farka amma cikin sujada([1])”.

2- Al-Kulayni ya nakalto wata ruwaya da take magana kan ibada Imam al-Askari (a.s), zuhudunsa da kuma amfani da lokacin da yake tsare a kurkuku wajen zikiri, ibada da komawa ga Allah Madaukakin Sarki, abin da ya yi tasiri ga mutanen da aka ba su aikin kulawa da kuma azabtar da shi, yana cewa:

“Wata rana Abbasiyawa sun shiga wajen Saleh bn Wasif, lokacin da aka tsare Abu Muhammad (Imam al-Askari), suka ce masa: Ka takura masa kada ka bar shi ya walwala….”.

Sai Saleh ya ce musu: ‘Me zan yi masa, bayan da na wakilta wasu mutane biyu masu tsananin kaushin zuciya (don kula da shi), amma sai suka koma mutane masu ibada, salla da azumi’.

Sai ya yi umarni da azo da wadannan mutane biyu, ya ce musu: Kaiconku! Me kuka sani dangane da wannan mutumin?

Sai suka ce masa: Me za mu ce kan mutumin da yake azumi da rana da daddare kuma ya tsaya da ibada, ba ya magana ba ya yin wani abu in ban da ibada, idan kuma ya kalle mu sai mu ji gabbanmu suna bari da kuma jin wani abu cikin zukatanmu da da ba mu da shi’.

Lokacin da Abbasiyawan suka ji haka, sai suka watse cikin fushi([2])”.

Irin lalacewar dabi'u, siyasa, yadda ake gudanar da al’amurra, zaluncin da ya yi yawa, fasadi da wasa da dukiyar al’umma da dai sauran nau’oi na zalunci da ta’addanci a kan al’umma da mahukunta suke yi, sannan a bangare guda kuma ga talauci da mummunan yanayin da al’umma suke ciki sakamakon ayyukan mahukunta, suna daga cikin abubuwan da suka sanya Imam al-Askari (a.s) ya nuna rashin amincewarsa da kuma wayar da kan al’umma kan irin wannan yanayi da ake ciki.

Wannan matsaya da Imam din ya dauka ta sanya mahukuntan lokacinsa, wato gwamnatin Mu’utaz, Al-Mahdi da ta al-Mu’utamid suka shirya don fuskantarsa da kuma takura masa rayuwa ta hanyoyi daban-daban.



([1]). Safinat al-Bihar na Al-Muhaddith al-Kummi, juzu’i na 1, shafi na 260.

([2]) A’ayan al-Shi’a na Muhsin Amin, juzu’i na 2, shafi na 41.