|
|
| |||
|
________________________
Imam al-Askari (a.s), kamar sauran iyaye da kakanninsa, ya
kasance wata alama ce da ba ta buya, Imami wanda babu wanda ya jahilce shi, ya
kasance malamin malamai, abin koyin masu ibada, jagoran addini da siyasa, wanda
ake nuni shi (da yatsa) kana kuma zukata suke komawa gare shi da so da kauna. Duk
kuwa da ta’addancin Abbasiyawa, adawa ta siyasa da Ahlulbaiti (a.s), azabtarwa
da takuran da mahukunta suke musu da mabiyansu da kuma sanya su a gidajen yari,
duk da irin wadannan abubuwa, to amma halifofin lokacinsa sun gaza wajen boye
matsayi da hakikaninsa ko kuma lalata matsayi da gudummawarsa ta ilmi da siyasa
bugu da kari kan matsayinsa na zamantakewa. Hakika ya samu daukaka da fifiko
sama da masu adawa da shi a zukatan al’umma. Ahmad
bn Abdullah bn Khakan, wanda yana daga cikin masu adawa da Imam al-Askari (a.s)
ya nakalto mana irin matsayi da daukakan da Imam din yake da shi na siyasa da
zamantakewa. Ibn
Shahr Ashub yana cewa:
“Husain
bn Muhammadu al-Ash’ari yana cewa, Muhammadu bn Aliyu yana cewa: An
Ban
taba gani daga gare su kamar abin da na gani a wajen Hasan bn Ali bn Muhammadu
bn Ridha ba, wata rana ya zo ya shiga wajen babana(đđ), ya ce: ‘Abu Muhammadu
bn al-Ridha ne yake sallama, sai ya ba shi izini ya kuma tarbe shi da zaunar da
shi a wajen sallarsa, ya ci gaba da yi masa magana da amfanar da shi har
lokacin da ya mike zai tafi, ya raka shi. Daga nan sai na tambayi babana
“Ya
dana! Wancan shi ne shugaban Rafidhawa(đđđ), da za a kwace halifanci
daga wajen Abbasiyawa, to da babu wani daga cikin Bani Hashim da ya cancanci
wanda matsayi kamarsa, saboda falalarsa, kamewa, azumi, salla, gudun duniya da
dai sauran halayensa.
Na
kasance na Sai
ya ce: Ban taba ganin mai yawan ilmi, mai yawan hakuri, mai yawan kamewa kamar
Hasan al-Askari ba([1])”.
Irin
wannan matsayi na Imam al-Askari (a.s) da matsayarsa ta siyasa
Yayin
da yake bayani
“Wata
rana mun taru a al-Askar (
Muna iya ganin matsayi da daukakan da Imam (a.s) yake da su
a zukatan al’umma idan muka yi dubi cikin wannan bayani da littattafan tarihi
suka ruwaito mana “Lokacin
da labarin wafatinsa ya watsu garin Samarra ya shiga wani irin hali na damuwa,
aka rufe shaguna, inda Bani Hasim, shuwagabanni, malamai, alkalai kai da sauran
al’umma gari duk suka nufi wajen jana’izarsa, a wannan ranar dai garin Samarra
ya cika makil da kuma tashin hankali kai ka ce tashin kiyama ne….([3])”.
(đ).
Kum: Wani gari ne daga cikin garuruwan kasar
(đđ). Babansa Abdullah bn Khakan ya kasance daga cikin ministocin sarki Mu’utamad al-Abbasi kana kuma na kurkusa da shi. |
||||