|
|
| |||
|
________________________
An haifi Imam
Hasan bn Aliyu al-Askari ne a garin Madina al-Munawwara a watan Rabi al-Thani
shekara ta 232 hijiriyya, kuma ana kiransa da al-Askari ne saboda wurin da suka
zauna tare da mahaifinsa Imam al-Hadi (a.s) da ake kira da Al-Askar (barikin
soji) a
Imam al-Askari (a.s) dai ya rayu da kuma girma
ne karkashin kulawar mahaifinsa Imam al-Hadi (a.s) wanda ya mallaki ilmi, gudun
duniya, jihadi da kuma aiki da ilmin da yake da shi, inda ya gaji dukkan wadannan
abubuwa daga gare shi. Ya rayu da mahaifinsa na tsawon shekaru ashirin da uku
da ‘yan wasu watanni, inda ya zamanto mai kokarin gyara al’umma da tabbatar da
su bisa tafarkin gaskiya kamar yadda iyaye da kakanninsa suka kasance.
Ruwayoyi daban-daban sun tabbatar da imamancin
Imam al-Askari (a.s) tun lokacin mahaifinsa al-Hadi (a.s).
“Abubakar al-Fahfaki ya ce: Abul Hasan
(al-Askari) (a.s) ya rubuta min cewa: “Dana Abu Muhammad
shi ne mafi ingancin zuriyar Manzon Allah, mafi tabbatacciyar hujja, shi ne
babba daga cikin ‘ya’yana, shi ne mai gado, kuma shi ne bangon hukumcin
Ahlulbaiti, ka tambaye shi dukkan abin da kake tambayana, don kuwa yana da
dukkan abubuwan da kake bukata([1])”. |
||||