|
|
| |||
|
________________________
Hakika Imam
al-Askari (a.s), kamar sauran madau-kakan iyaye da kakanninsa (a.s), ya
fuskanci zalunci da takurawa sakamakon gwagwarmayarsa ta siyasa wajen fuskantat
zalunci da ta’addancin mahukunta, kana kuma don kare asasin sakon Musulunci mai
tsarki, a matsayin babban nauyin da ke kansa na jagoranci da shiryar da mutane
da Allah Madaukakin Sarki ya dora masa.
Wannan nauyi dai ya sanya su (Imamai) cikin
mawuyacin hali na tsawon lokaci, sun fuskanci tsarewa a gidajen yari da kuma
kisan gilla, kamar yadda za mu gani cikin wadannan ruwayoyi masu zuwa:
1-
Sarki Mu’utaz ya tsare Imam al-Askari (a.s) tare
da Abu Hashim al-Ja’afari tare da wasu daga cikin mabiyan Ahlulbaiti (a.s).
2-
Abu Hashim Dawud bn al-Kasim ya
“Na kasance
cikin gidan yarin da aka fi sani da gidan yarin Saleh bn Wasif al-Ahmar ni da
Hasan bn Muhammadu al-Akiki da Muhammadu bn Ibrahim al-Umri da wane da wane,
sai aka shigo mana da Abu Muhammad al-Askari (a.s) da dan’uwansa Ja’afar, sai
muka koma yi masa hidima. Mai kula da tsare shi kuwa shi ne Saleh bn Wasif,
kuma akwai wani mutumi tare da mu wanda ya ce shi mabiyin Ahlulbaiti ne.
Sai Abu Muhammad (a.s) ya juyo ya ce:
“Da
ba don akwai wani a cikinku da ba ya tare da ku ba, da na
Sai ya yi ishara wa wannan mutumin da ya fita,
bayan da ya fita, sai ya ce mana: “Wannan mutumin ba daga cikinku ya ke, don
haka ku yi hankali da shi, a cikin tufafinsa akwai takardar da ya rubuta dukkan
abubuwan da kuke fadi
Sai suka tashi suka binciki tufafinsa, sai kuwa
ga takardar da ya rubuta dukkan abubuwan da suka ce([1])”.
3- Har ila yau al-Tabrisi ya ruwaito cikin
littafinsa A’alam al-Warah daga wasu maruwaita cewa:
“Ahmad bn Muhammad, ya ce: Na rubuta wa Abu
Muhammad (a.s) wasika lokacin da al-Muhtadi ya fara kashe masoya Imam Ali
(a.s), inda na ce: Ya shugabana! Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya shagaltar
da shi daga gare ka, na samu labarin cewa yana nan yana maka barazana, yana
cewa ‘wallahi, sai na shafe su daga doron kasa’. Sai ya rubuto min da hannunsa
ya ce:
“Ai kwanakinsa sun kusan karewa, daga yau din
nan ka kirga kwanaki biyar, a kwana na shida za a kashe shi cikin wulakanci”,
kuma
hakan ya faru kamar yadda ya ce([2])”.
Kamar yadda al-Muhtadi ya ke tunanin kashe Imam
(a.s), gabanninsa ma al-Mu’utaz ya yi wannan tunani da kuma shirya hakan, kamar
yadda Ibn Shahr Ashub ya ruwaito:
“Al-Mu’utaz ya bukaci Sa’id al-Hajib da ya tafi
da Abu Muhammad (a.s) zuwa Kufa kana ya sare wuyansa a
4- Shaikh al-Mufid ya ruwaito cewa: “An mika Abu
Muhammad (a.s) hannu Nahrir, wanda ya kan azabtar da shi da kuma kuntata masa,
wata rana sai matarsa ta ce masa: ‘Ka ji tsoron Allah, don kai ba ka san wane
ne a gidanka ba’, sai ta fara gaya masa falaloli da ibadunsa (a.s), sai ta ce
masa: “Lalle ni ina ji maka tsoronsa([4])”.
5- Har ila yau al-Mufid ya ruwaito daga
Muhammadu bn Isma’il al-Alawi cewa: “Wata rana an tsare Abu Muhammadu (a.s) a
wajen Aliyu bn Awtash, wanda ya kasance mai tsananin adawa da Ahlulbaiti (a.s).
sai aka ce masa: Ka aikata duk abin da za ka aikata da shi, sai ya ce: Kwana
guda bai cika har sai da ya fara girmama shi, ba ya daga ido ya kalle shi don
girmamawa. Kafin fitan Imam, sai da ya kasance mutumin kirki kana kuma wanda ya
fi kowa fadin alheri dangane da shi([5])”. |
||||