Ana kirga kimar duk wani aiki na addini ko kuma na siyasa ne da irin tasiri da kuma sakamako na alherin da ya haifar da kuma canjin da ya kawo wajen gina rayuwar dan'Adam da kuma al'umma gaba daya. Akwai yiyuwar wannan tasiri da sakamako su banbanta saboda yanayi na siyasa da kuma lokaci kamar yadda kuma sukan iya kasance su dau wani lokaci mai tsawo ko kuma gajere kafin a ga tasirin. Akwai kuma yiyuwar tasiri da sakamakon su kasance ne a kan wani lamari na siyasa ko na zamantakewa ayyanannu ko kuma na wani lokaci kawai gwargwadon yanayi ko kuma zamanin da suka sami kansu, kamar yadda kuma sukan iya kasancewa fadaddu da suka mamaye ko ina ko kuma akasin hakan, da dai sauransu.
To don haka, wannan yunkuri na Imam Husain (a.s) ya kasance yunkuri ne mai girman gaske, ma'abucin kima da tasiri, mai fadaddiyar manufa, don kuwa manufarsa ba wai kawai ya takaita ne ga samun mulki da hukuma ba, duk kuwa da cewa dai Husaini (a.s) din ya yi amanna da cewa samun karfi irin na mulki wani wajibi ne na siyasa wajen kawo canji cikin al'umma, to amma dai manufarsa ba wai kawai ta takaita ga hakan ba ne. Imam Husain (a.s) ya kasance ma'abucin manufa mai girman gaske kana fadaddiya na kurkusa da na nesa, yana kallon mulki ne a bisa akidar da Mahaifinsa ya tabbatar:
"Ya Allah Ka san cewa abin da muke kokarin yi ba gasa ce don neman mulki ba, ko kuma neman mallakan dan abin da ya rage na abin duniya ba. Face dai abin da muke son yi shi ne dawo da alamun addnininKa da suka bace, mu raya dokokinKa da aka mance da su da kuma kare wadanda ake zalunta daga cikin bayinKa".
Hakika Imam Husain (a.s) yana son ne ya cimma wasu manufofi ta hanyar wannan yunkuri nasa, kamar:
1- Kawo canji cikin harkokin siyasa da kuma tsarin mulki da gudanarwa ta siyasa, bugu da kari kan mu'amala da al'umma gwagwardon dokoki da mizanin da Musulunci ya tabbatar da su.
2- Wayar da kan al'umma a bangaren siyasa da kuma mayar da su masu sa ido cikin lamurran gudanar da mulki don kada a kauce wa dokokin Musulunci.
3- Tabbatar da halalcin amfani da karfi a kan azzalu-min shugaba.
4- Sake gina al'umma bisa ingantaciyyar tarbiyya.
5- Gyara kura-kuran da aka yi da kuma gudanar da shari'a da dokokinta.
6- Karya shamakin tsoro da fargaba da aka kafa wa al'umma da kuma motsa lamirin yunkuri da sadaukarwa tsakanin al'umma.
Mikewar Imam Husain (a.s) ke da wuya - duk da ya san da wuya wannan yunkuri na sa ya samu nasara ta soji face dai zai kasance ne wani mataki na farko na motsawar al'umma da kuma samun ruhin yunkuri - da sadaukarwar da suka yi sai ga shi wannan hukuma ta Umayyawa ta fara jijjiguwa da nufin faduwa kasa warwas. Don ta fara rasa alakar da take da shi da al'umma, duk kuwa da kokarin da ta yi na amfani da karfi da sauran nau'o'i na ta'addanci wajen kwantar da al'umm, amma al'ummomi sai nuna alamun bore su ke yi, sun fara jin shu'urin laifin kashe Imam Husain (a.s) da aka yi. Ko ina sai ruhin yunkuri da gwagwarmaya ta makamai don raunana da kuma kawar da gwamnatin Umayyawa ka ke gani, lamarin da daga karshe dai ya kawo faduwar gwamnatin Umayyawan warwas, hakan kuwa ya biyo bayan wannan yunkuri na Husaini (a.s) ne da kuma jininsa da na mabiyansa da suka zuba a kasar Karbala.
A matsayin misali, wannan yunkuri na Imam Husain (a.s) ya share fage wa Abdullah bn Zubair a Makka wajen yunkurin da kuma kawar da gwamnatin Umayyawa.
Littattafan tarihi sun rubuto wasu daga cikin abubuwan da suka faru, wadanda suke nuni da tasiri da kuma sakamakon wannan yunkuri na Husain (a.s).
Al-Ya'akubi cikin Tarihinsa ya ce: 'Wani mutum ya ce: Wata rana na tafi wajen Abdul Malik bn Marwan, sai na gan shi tare da kan Mus'ab bn al-Zubair, sai na ce masa: 'Ya Amiral Muminina, hakika na ga wani abin mamaki a wannan guri', sai ya ce: 'Me ka gani'?, sai ya ce: 'Na ga kan Husaini bn Ali (a.s) a gaban Ubaidullah bn Ziyad, sannan kuma na ga kan Ubaidullah bn Ziyad a gaban al-Muktar bn Ubaidah, sannan kuma na ga kan Al-Mukhtar bn Ubaidah a gaban Mus'ab bn al-Zubair, to yanzu kuma ga shi na ga kan Mus'ab bn sal-Zubair a gabanka(1)'.
Mutanen Madina sun kaddamar da yunkuri da bore a kan Yazid da gwamnansa Usman bn Muhammad bn Abi Sufyan, inda suka kore shi daga garin da dukkan Umayyawa. Wanda ya jagoranci wannan bore na mutanen Madina dai shi ne Abdullah bn Handhalah bn Abi Aamir (wanda Mala'iku suka wanke shi). Sai dai daga baya sojojin mutanen Sham sun kawo hari garin Madinan(2) inda suka keta huruminsa da zubar da jinin mutanensa. Al-Ya'akubi ya yin da yake siffanta wannan abin da ya faru a Madina da kuma yunkurin mutanen cewa ya ke yi:
"An kashe adadi mai yawa na mutanen (garin) da kuma keta hurumin Manzon Allah (s.a.w.a) da halalta wa sojojin Umayyawa garin ta yadda an samu budurwayen da suka haifi jariran da ba a san ubanninsu ba, don haka aka tilasta wa mutane mika mubaya'arsu ga Yazid bn Mu'awiyyah a matsayin bayi(3)".
Wadannan abubuwa dai da suka faru za su nuna mana irin yadda al'umma suke ganin Yazid, kamar yadda kuma suke tunasar mana da fadin Abdullah bn Muti' ga Imam Husain (a.s): "Na rantse da Allah, idan har aka kashe ka to za a mai da mu bayi bayanka".
Bayan wani lokaci dai an fara samun yunkuri da mayar da martanoni da suke kira zuwa ga daukan fansar jinin Husaini (a.s) ta yadda Husaini (a.s) ya kasance wani take na siyasa kana kuma karfi mai motsawa cikin tarihin gwagwarmaya da fada da zalunci. Lamarin dai ya soma ne da yunkuri Al-Tawwabun (Tubabbu) a garin Kufa karkashin jagorancin Sulaiman bn Sird al-Khuza'i da Musayyab bn Najbah al-Fazari, inda suka daga taken tuba da tunani kan gazawar da suka yi wajen taimakon Imam Husain (a.s) ta hanyar yakan Umayyawa da neman fansar jinin Husaini (a.s).
Daga nan kuma sai yunkurin al-Mukhtar bn Ubaidah al-Thakafi da Ibrahim bn Malik al-Ashtar a shekara ta 66 B.H., suna masu rera taken "Daukan Fansar Jinin Husaini". Sun sami nasarar ritsawa da wadanda suka kashe Husaini (a.s) inda suka kashe Ubaidullah bn Ziyad, Husayn bn Numayr da Umar bn Sa'ad.
Wannan ruhi na gwagwarmaya da yunkuri dai ya ci gaba har lokacin da gwamnatin Umayyawa ta fadi a hannun masu yunkurin Abbasiyawa, wadanda a zahiri suke kira zuwa ga mayar da al'amurra ga Ahlulbaitin Manzo (s.a.w.a).
Ta haka ne dai jinin Imam Husain (a.s) ya kunna wutan yunkuri da bore wa hukumar Umayyawa da kawo karshen kasantuwansu a fagen siyasa har aka kawo karshensu dai gaba daya. Babu shakka Husaini (a.s) zai ci gaba da kasancewa taken ma'abuta yunkuri kana kuma fitila ga ma'abuta 'yanci sannan makaranta ta gwagwar-maya da kuma 'yanto al'umma.
Aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi da ranar da ya yi shahada da kuma ranar da za a tashe shi rayayye.
"Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai"