Hakika shari'ar Musulunci dai ta tsara yanayin yadda siyasa za ta kasance, ta kuma sanya ta karkashin tubalin akida, dabi'u na kwarai da kuma tsararrun dokoki, haka nan kuma ta dora yarjejeniyoyi da kuma alkawurran da aka yi a kan wani matsayi na musamman.
Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
( يا أَيُّهَا الَّذينَ ءامَنواْ أَوْفُواْ بالعُقُودِ ) "Ya ku wadanda suka yi imani! Ku cika alkawura". (Suratul Ma'ida: 5:1)
( وأوْفُوا بالعَهْدِ إنَّ الْعَهْدَ كَانَ مَسْؤولاً ) "Kuma ku cika alkawari. Lalle alkawari ya kasance abin tambayawa ne". (Suratul Isra': 17:34)
Hakika Limaman Ahlulbaiti (a.s) sun kasance abin koyi ne wajen kula da kyawawan dabi'u da kuma dokoki, halaye da dabi'unsu na siyasa sun kasance daidai da yadda siyasar Musulunci ta tsara. Lalle siyasar "manufa ta kan tsarkake tafarki" ba ta kasance tushen siyasarsu ta mu'amala ba a lokacin da suke mu'amala da al'umma ko kuma ma da abokan gabansu. Ba su kasance masu bambance tsakanin siyasa da dabi'a ba, don kuwa Musu-lunci yana ganin dole ne siyasa ta kasance a bisa tubalin ibada da kyawawan dabi'u. Don haka ne ma Imam Husaini (a.s) ya ki amincewa da bukatan da mutanen Iraki, wadanda suka kasance mabiya Ahlulbaiti ne, wadanda kuma suke dandanan dacin zalunci Umayyawa saboda son da suke wa Ahlulbaitin, suka gabatar masa, bayan shahadar Imam Hasan (a.s), na ya jagorancesu wajen kawar da Mu'awiyya ba, saboda akwai alkawari da yarjejeniya tsakaninsa da Mu'awiyya, wato yarjejeniyar da Imam Hasan ya sanya hannu kanta shi da Mu'awiyya, don haka ba ya halalta ya keta wannan yarjejeniya.
Shaikh al-Mufid ya nakalto wannan kyakkyawar matsaya da kuma dabi'a ta kwarai ta Imam Husaini (a.s) inda ya ke cewa:
"Wannan shi ne abin da al-Kalbi da al-Madani da sauran malaman tarihi suka ruwaito cewa: Lokacin da Hasan ya rasu, 'yan shi'an kasar Iraki sun rubuta wa Husaini (a.s) suna bayyana masa kudurinsu na yi masa mubaya'a da kuma kawar da Mu'awiyya, amma ya ki amincewa da wannan bukata tasu, yana mai cewa akwai alkawari da yarjejeniya tsakaninsa da Mu'awiyya, kuma baya halalta a gare shi ya keta ta har sai lokacin da aka diba mata yayi, wato lokacin da Mu'awiyya ya mutu(1)".