GUDUMMAWAR IMAM HUSAINI (A.S)

Mu'awiyya ya yi kokarin ganin bayan duk wata matsala da take fuskantarsa da kuma fuskantar wannan buri na sa na nada dansa a matsayin halifa ta hanyar ba da cin hanci (kudi) ga wasu mutane, wayo da kuma ta'addanci, daga nan kuma sai ya mika mulkin al'umman musulmi zuwa ga dansa Yazid. To sai dai kuma duk da hakan Umayyawan ba su sami kwanciyar hankali ba kan yadda al'amurra suke gudana, don kuwa sabon sarkin da aka nadan ya gagara shawo kan al'umma da kuma lalata mata akidunta, don kuwa tuni Manzon Allah (s.a.w.a) ya riga da ya gina ta a kan soyayya ga Mutanen gidansa, kamar yadda Alkur'ani mai girma kuma ya riga da ya dasa ruhin wayewa ta siyasa cikin zuciyarta. Don haka wannan al'umma ta riga da ta san siffofin shugaba, tana kuma iya bambance shaksiyyar shugaba, haka nan kuma ta san hakkokinta na siyasa, ta kuma san gudummawar da za ta iya bayarwa cikin tarihi, don haka ne ta ki amincewa da wannan mulkin na danniyar da aka dora mata.

Babu shakka shekaru ashirin na mulkin danniyar Umayyawa, da kuma yadda take wasa da dukiyar al'umma, mukami da kuma mulki, ya isa kawai ya sanya al'umma su mike tsaye wajen kawar da gwamnatin Yazid dan Mu'awiyya wanda aka dora shi a kansu. A dabi'ance dai a duk lokacin da al'umma take fuskantar zalunci da babakeren mahukunta, ba abin da take dubi da kuma komawa gare shi face manyan mutanen da suke adawa da wannan hukuma, sanannun mutane wadanda suke da ruhin yunkuri, wadanda za su fitar da su daga wannan hali da suke ciki. To a wancan lokacin kuwa, al'ummar ba ta da wani mutum da za ta dogara da shi kamar Imam Husaini bn Ali bn Abi Talib (a.s), wanda yake shi ne shugaban Kuraishawa kana kuma jikan Ma'aiki (s.a.w.a), dan Amirul Muminina, mafi daukakan al'umma wajen ilmi, kyawawan dabi'u da kuma tsantsaini. Hakika al'umma ba su da wani wanda ya fi shi, kuma sun riga da sun san yadda yake adawa da yin mubaya'a wa Yazid da kuma nada shi da babansa ya yi a matsayin halifa, kai face ma dai Mu'awiyya ya kasance yana tsoronsa, da kuma sanin cewa yana da karfin jagorantar al'umma da kuma motsa ruhinsu wajen fuskantar Umayyawan.

Haka nan kuma Yazid, shi ma, ya san irin karfafaffiyar alakar da take tsakanin al'umma da Imam Husaini (a.s), da kuma irin ruhin yunkurin kawo sauyi da ke tattare da shi. Haka nan kuma ya san matsayarsa dangane da Mu'awiyya da kuma yadda yake tsananin adawa da yadda Mu'awiyyan ya dora shi akan al'ummar musulmi. Don haka, dukkan himmarsa da kuma tsoronsa ya mai da su kan Imam Husaini (a.s), saboda da haka hawansa mulki ke da wuya sai ya rubuta wasika zuwa ga Walid bn Utba bn Abi Sufyan, wanda yake shi ne gwamnan Madina, yana mai ce masa:

"Bayan haka, ka karbi bai'a daga gurin Husaini, Abdullahi bn Umar da kuma Ibn Zubair, kuma kada ka bata lokaci wajen yin hakan(1)".

Lokacin da wannan wasika ta shiga hannun Walid ya ga abin da ke cikin na batun mutuwar Mu'awiyya(2), nada Yazid a matsayin halifa da kuma nauyin da aka dora masa na karbar bai'a daga wajen wadannan mutane da aka ambata, sai ya boye wannan batu bai gaya wa kowa abin da wasikar ta kumsa ba, har sai ya yi tunani. Bayan dan tunani sai ya kira Marwan don bayyana masa abin da ake ciki da kuma neman shawararsa kan yadda za a fuskanci Husaini (a.s) da wannan bukata ta Yazid tun kafin al'amari ya fita daga hannunsu. Ba wata shawara dai da Marwan ya bayar in ban da ayi amfani da karfi da kuma tilasci, yana mai cewa:

"Ni ina ganin babu abin yi face ka kira su yanzu ka umarce su da yin mubaya'a, idan sun aikata haka, to ya wadatar musu, idan kuwa sun ki, to ka sare wuyayensu tun kafin ma su san batun mutuwar Mu'awiyya. Don kuwa idan har suka sami labarin mutuwar Mu'awiyya, to fa kowannensu zai koma waje guda ne don yin adawa da halifa da kuma kiran mutane zuwa ga kansa. Lalle Ibn Umar kan ba ya son yaki, ba zai so ya mulki mutane ba face cikin ruwan sanyi(3)".

Nan take aka gama wannan shawara, aka tsara yadda za a fuskanci wannan matsala. Saboda haka sai aka fara da Imam Husaini (a.s) ta hanyar kangewa da kuma kewaye shi, don ma kada labarin mutuwar Mu'awiyya ya isa ga mutane, su koma ga Husaini (a.s) don yi masa bai'a a matsayin jagoransu.

"Don haka sai Walid ya tura Abdullahi bn Umar bn Usman, wanda yaro ne, don ya kira masa Imam Husaini (a.s) da kuma Ibn Zubair, ko da zuwa sai ya same su a masallaci suna zaune. Sai ya ce musu su zo Walid yana kiransu amma fa lokacin ba lokaci ne da Walid yake sauraran mutane ba, sai suka ce masa tafi muna zuwa(4)".

Hakika wannan kira dai ba lafiya ba, kuma babu yadda za a yi Husaini (a.s) ya gafala ga hakan, shin me ya faru ne? Me Walid yake so?

Lalle Imam Husaini (a.s) da Ibn Zubair dai sun fara jin hatsarin dake tattare da wannan kira, sun fahimci cewa lallai akwai wani sabon abu da ya faru, idan ba haka ba kuwa to mene ne dalilin wannan kira? Kuma me ya sa a wannan lokaci da ba al'adar Walid ba ne ya gana da jama'a? Don haka sai Ibn Zubair ya tambayi Imam Husaini (a.s) cewa: "Wani dalilin ne kake gani ya sa ya kira mu a wannan lokaci da ba ya ganawa da jama'a a cikinsa? Sai Husaini (a.s) ya ce: "Ina tunanin dagutunsun nan ne ya mutu, don haka ya kira mu don karbar bai'a daga gare mu kafin labarin mutuwar ta isa ga mutane". Sai Ibn Zubair ya ce: Lallai ni ma ba na ganin akwai abin da ya wuce hakan, to me kake tunanin yi?

Sai Imam Husini (a.s) ya ce: "Zan tara mabiya na, mu tafi gurinsa, su tsaya a bakin kofa ni kuma in shiga wajensa".

Sai Ibn Zubair ya ce: Lallai ni ina maka tsoron shiga wajensa.

Sai Imam Husaini (a.s) ya ce: "Hakika ba zan shiga wajensa face sai na san zan iya kare kaina daga dukkan sharrinsa(5)".

Ta haka ne Imam Husaini (a.s) ya fuskanci wannan makirci na Umayyawa, yana sane da bukatar da ake da shi na daukan matakin gaggawa da kuma hanyar da ya kamata abi wajen fuskantarsu.

"Hakika ba zan shiga wajensa face sai na san zan iya kare kaina daga dukkan sharrinsa".

Ta haka ne Imam Husaini (a.s) ya shiryawa fuskantar wannan mulki na Yazid cikin jarunta da karfin ruhi, da kuma fuskantar wannan yanayi na siyasa mai tsananin hatsarin gaske. Lalle ya riga da ya san wane ne Yazid da kuma cikakken sanin halaye, ruhi da kuma siyasarsa, kamar yadda kuma ya san cewa kawar da shi yana bukatan sadaukarwa da zubar da jini.

Don haka, sai Imam Husaini (a.s) ya kira 'yan'uwansa da mutanen gidansa, suka kewaye shi, adadinsu kuwa ya kai mutane talatin, dukkanninsu kuwa jarumai ne ma'abuta sadaukarwa da yunkuri. Sai ya nufi gidan Walid tare da wadannan mutane wadanda suke shirye don su kare kansu da kuma fuskantar duk wata barazana da ka iya fuskantarsu. A daidai wannan lokaci dai babu alamar yarda a tattare da Imam Husaini (a.s), kamar yadda kuma babu wata alama ta rauni da sassauci a harshensa, yana tare da zuciyar Aliyu bn Abi Talib, a hannunsa kuwa ga takobin gaskiya, ga shi kuma yana tare da numfashin annabci, daukakar imamanci da kuma girman mazantaka. Husaini ya tafi ne don ya ayyana matsaya, ya kuma sanar da mataki, ya kawo karshen ka-ce-na-ce, ya kuma fadi kalmar rashin yarda yana mai bayyana matsayar al'umma, da kuma bayyana harshen shari'a, alhali yana tare da jaruman mutane, ma'abuta sadaukarwa da kuma kawo canji.

Ta haka ne Imam Husaini (a.s) ya isa fadar Walid a lokacin kuwa Marwan bn Hakam yana nan, aka bude masa kofa, sai ya ajiye mutanensa a wajen da za su iya ganinsa da kuma jin kalamansa don su kawo masa dauki idan bukatar hakan ta taso. Yana mai ce musu:

"Idan na kira ku ko kuma kuka ji na daga sautina to dukkanku ku shigo don kawo min dauki, idan kuwa ba haka ba to ku dakata har sai na dawo(6)".

Daga nan sai Husaini (a.s) ya shiga fadar Walid alhali Marwan bn Hakam yana tare da shi, ya yi musu sallama kana ya zauna. Sai Walid ya fara magana, ya sanar da shi batun mutuwar Mu'awiyya da kuma bukatar ya yi mubaya'a wa Yazid, sai ya ce masa:

"Ya kai Sarki! Ai ba a yin mubaya'a a boye, ai sai ka kira mutane gobe ni ma sai ka kira ni in zo".

Nan take sai Marwan ya tsoma baki ya ce: Yallabai! Kada ka yarda da wannan bukata tasa, idan ba zai yi ba ka sare wuyansa. Nan take sai Imam Husaini (a.s) ya fusata ya ce masa:

"Kaiconka, Ya kai dan bakuwar mace! Kai ne za ka sare wuya na, wallahi karyarka kuma ka nuna asalinka".

Daga nan sai ya dubi Walid ya ce:

"Ya kai Sarki! Hakika mu ne mutanen gidan Annabci, mabubbugar sako, wadanda mala'iku sukan zo musu, da mu Allah Ya bude da mu kuma Ya rufe. Yazidu kuwa mutum ne fasiki, mashayin giya, mai kashe ran da aka haramta, mai bayyana fasikanci a fili, kama ta lalle ba zai yi wa kamarsa bai'a ba. To amma da safe da ni da ku za mu ga wane ne tsakaninmu ya cancanci halifanci da kuma mubaya'a". Daga nan sai ya fita.

Sai Marwan ya ce wa Walid: Lalle ka saba min. sai ya ce masa: Kaiconka, lallai kai ka zaba min abin da zai kawar min da addinina da kuma duniyata, wallahi ba na son a ba ni duniya da abin da ke cikinta sakamakon kashe Husaini. Wallahi ba na tsammanin mutum zai gana da Allah lafiya ranar tashin kiyama alhali yana dauke da jinin Husaini, lallai Allah ba Zai kale shi, kuma ba Zai tsarkake shi ba, kuma yana da azaba mai tsanani(7)".

Ta haka ne aka kawo karshen wannan taro, Imam Husaini (a.s) kuma ya koma cikin mutanensa yana mai shirin jihadi da kuma sanar da mutane wannan kuduri nasa, da kuma cewa ya dauki garin Makka a matsayin mafarar wannan yunkuri.




____________
(1)- Tarikh al-Umam wal Muluk na Tabari, juzu'i na 4, shafi na 250, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 14.
(2)- Mu'awiyya ya mutu ne a watan Rajab shekara ta 60 Hijiriyya.
(3)- Tarikh al-Umam wal Muluk na Tabari, juzu'i na 4, shafi na 251, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 14.
(4)- Tarikh al-Umam wal Muluk na Tabari, juzu'i na 4, shafi na 251, Al-Kamil fi al-Tarikh na Ibn Athir, juzu'i na 4, shafi na 15.
(5)- Kamar na sama.
(6)- Kamar na sama da kuma Al-Fusul al-Muhimma na Ibn al-Sabbagh al-Maliki, shafi na 182.
(7)- Maktal al-Husaini na Ibn Dawus, shafi na 10 da 11. Haka nan Tabari ma ya kawo wannan labari cikin Tarikh al-Umam wa al-Muluk, juzu'i na 4, shafi na 251 da kuma Ibn Athir cikin Al-Kamil fi al-Tarikh, juzu'i na 4, shafi na 15.